logo

HAUSA

‘Yan siyasar Amurka, ku daina kalubalantar al’ummar Sinawa

2021-10-28 11:25:08 CRI

‘Yan siyasar Amurka, ku daina kalubalantar al’ummar Sinawa_fororder_微信图片_20211028112348

A ranar 26 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya fitar da sanarwa, inda ya yi shelar “nuna goyon baya ga Taiwan wajen shiga tsarin MDD”. Kafin wannan, a ranar 25 ga wata, aka cika shekaru 50 da dawo wa jamhuriyar jama’ar Sin halastacciyar kujerarta a MDD. Yadda Amurkar din ta hura wutar batun matsayin Taiwan a MDD a daidai wannan lokaci, ya shaida mummunar manufar da take neman cimmawa.

A yayin da shugabannin kasashen biyu suka tattauna ta wayar tarho a watan Satumban wannan shekara, Amurka ta ce ba ta da niyyar canza matsayinta game da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Ya zuwa watan da muke ciki, yayin da manyan jami’an kasashen biyu ke shawarwari a birnin Zurich, Amurka ta sake jaddada bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. To, game da yadda ta nuna fuska biyu a kan wannan batu, lalle ta nuna cewa ita kasa ce mai cin amana.

Sanin kowa ne cewa, kasa mai mulkin kanta ne kawai ke iya shiga MDD, kuma jamhuriyar jama’ar Sin ita ce halastaciyyar gwamnati kadai dake iya wakiltar al’ummun Sin. Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma dole ne ta bi ka’idar Sin daya tak a duniya a yayin da take halartar harkokin kungiyoyin kasa da kasa.

A zahiri dai Amurka tana son neman shawo kan kasar Sin bisa batun Taiwan. Sai dai batun Taiwan yana shafar ainihin moriyar kasar Sin, kuma ba za a taba lamintar yadda ake kalubalanci manufar Sin daya tak a duniya ba. Muna bukatar Amurka ta gyara kuskurenta nan da nan, ta daina kalubalantar al’ummar Sinawa. (Lubabatu)