logo

HAUSA

Sin Ta Kuduri Aniyar Cika Alkawarin Ta A Fannin Dakile Sauyin Yanayi

2021-10-28 16:59:59 CRI

Sin Ta Kuduri Aniyar Cika Alkawarin Ta A Fannin Dakile Sauyin Yanayi_fororder_2

A shekarun baya bayan nan, hankulan sassan kasa da kasa na kara karkata ga batun daukar matakan da suka wajaba, na dakile mummunan tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa rayuwar bil adama.

Masana da dama na ci gaba da bayyana illar kin daukar matakan da suka wajaba, game da dakile sauyin yanayi, duba da irin bala’u da hakan ke haifarwa, da ma wadanda ke tafe idan har ba a gaggauta aiwatar da matakan da suka kamata ba.

A wannan karni da muke ciki, bil adama na ci gaba da fuskantar kalubale daban daban ta fuskar sauyin yanayi, kama daga karuwar zafi, da ambaliyar ruwa, da mahaukaciyar iska mai daidaita yankuna, zuwa matsalar fari, da bacewar wasu halittu daga doron duniya.

Hakan ne ma ya sa kasashe da dama, ke ta hankoron sauke nauyin dake wuyan su, game da matakan dakile sauyin yanayi. Game da hakan ne, a ranar Laraba, majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da muhimmiyar takardar bayani, mai kunshe da irin nasarorin da kasar ta cimma a fannin dakile sauyin yanayi, tare da raba fasahohin ta, da dabarun da take aiwatarwa tare da sauran kasashen duniya a fanni.

Wannan takarda wadda ta kunshi sassa 4, ta yi bitar irin sabbin matakan da kasar Sin ke aiwatarwa, don cimma nasarar wannan muhimmin aiki, da kuma dabarun kasar a matakin hukuma, da sauye sauye da kasar ke aiwatarwa, tare da rawar da take takawa wajen gina tsarin jagoranci a matakin kasa da kasa da na shiyyoyi, domin kaiwa ga nasarar dakile tasirin sauyin yanayi.

Ko shakka ba bu, matakai irin wadannan da mahukuntan Sin ke dauka, na alamta irin muhimmanci da kasar ke dorawa kan sha’anin dakile sauyin yanayi. Kuma hakan wani abun koyi ne ga sauran sassan duniya, musamman kasashe masu wadata, da a ko da yaushe ke daukar alkawuran mara baya ga manufofin yaki da sauyin yanayi, yayin da wasu daga cikin su kan gaza cika alkawuran na su yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)