logo

HAUSA

Kasar Togo ta karbi sabon rukunin alluran rigakafin Sinovac na kasar Sin karkashin shirin COVAX

2021-10-27 09:46:03 CRI

Kasar Togo ta karbi sabon rukunin alluran rigakafin Sinovac na kasar Sin karkashin shirin COVAX_fororder_211027-yaya 2-Togo

Ma'aikatar lafiya ta kasar Togo, ta sanar a shafinta na Twitter jiya Talata cewa, kasar ta karbi alluran rigakafin Sinovac na kasar Sin guda 702,000 karkashin shirin COVAX.

Ministan lafiya na kasar Togo Moustafa Mijiyawa ne ya karbi sabon rukunin rigakafin a filin jirgin saman Gnassingbe Eyadema, a gaban wakilan hukumar lafiya ta duniya (WHO) da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) dake kasar.

A cewar ma’aikatar, alluran rigakafi guda 702,000, sun kasance kashi mafi girma na alluran rigakafin da kasar ta samu karkashin shirin na COVAX tun daga Maris 2021, lokacin da shirin ya fara samar da alluran rigakafin ga kasar. Ya zuwa yanzu, yawan adadin alluran kamfanin Sinovac na kasar Sin da kasar ta karba kai tsaye ta hannun shirin COVAX ya kai 1,027,000.

Wannan wani babban ci gaba ne ga hukumomin kiwon lafiyan kasar, wanda zai bunkasa dabarun gwamnati da ke fatan yiwa a kalla kashi 60 cikin 100 na al'ummar kasar riga kafi. (Ibrahim)