Shugaban POA: Gasar Olympics ta Beijing dake tafe za ta zama zakaran gwajin dafi
2021-10-27 10:25:22 CRI
Shugaban hukumar shirya gasar Olympic ta Pakistan ko POA a takaice Mr. Syed Arif Hasan, ya ce bisa kwarewar kasar don gane da yadda ta tsara gasar Olympics ta birnin Beijing a shekarar 2008 cikin nasara, kwazon ta a fannin shirya gasar zai taimaka wajen cimma nasarar gudanar da gasar lokacin hunturu ta Beijing dake tafe a shekarar 2022.
Syed Arif Hasan ya ce kasa da watanni 4, birnin Beijing zai karbi bakuncin wannan gasa, inda zai zamo birni na farko a duniya da zai karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin zafi da kuma hunturu, wanda hakan babbar nasara ce. Hasan ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Jami’in wanda ya kasance daya daga wadanda suka kewaya da wutar gasar Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 a Pakistan, ya kuma kasance daya daga ‘yan tawagar kasar Pakistan da suka halarci gasar ta birnin Beijing, ya ce wannan babbar gasa dake tafe an shirya ta yadda ya kamata, kuma gogewar Sinawa wajen tsara sassan gasar zai baiwa kasar karfin gwiwa na cimma gagarumar nasara a gasar ta badi dake tafe, ta yadda ‘yan kallo da ‘yan wasa daga dukkanin sassan duniya za su gamsu da gasar.
Ya ce yana dokin zuwan wannan lokaci, domin ya halarci gasar ta Beijing ta 2022, duba da yadda ya nishadantu da wadda aka gudanar a Beijing din a shekarar 2008.
Jami’in ya ce "An kawata birnin Beijing, an yi amfani da dogon tarihin birnin Beijing don fayyace tarihin kasar Sin, an kuma nuna wasanni masu ban sha’awa...Na halarci bikin bude gasar. Ba zan iya bayyana yadda na ji ba don gane da kyawun gasar. Kuma hakan ne yasa nace, akwai tabbacin masu shirya gasar dake tafe a lokacin hunturu za su baiwa duniya mamaki. Muna fatan ganin wannan lokaci”.
Game da ayyukan shirya gasar, da suka kunshi gwajin wasannin hunturu, hasan ya ce ba abu ne mai sauki kammala dukkanin wadannan ayyuka alhali ana tsaka da tunkarar cutar COVID-19 ba, amma duk da haka, wannan gasa dake tafe za ta gudana cikin nasara, duba da kwarewar masu shirya ta. Ya ce yana da kwarin gwiwa, cewa gasar dake tafe ita ma za ta zamo zakaran gwajin dafi."
Hasan ya ce "A gani na ba wani abun damuwa ko kadan, domin mun ga yadda Sin ta tsara komai. Kuma ina ga ba wanda zai nuna damuwa kan shirin da ake yi..ba wata matsala, domin an kammala dukkanin shirye shirye da suka wajaba. Kaza lika sauran masu ruwa da tsaki su ma sun ba da ta su gudummawa, wajen tabbatar da nasarar tsarin da aka tanada, komai ya daidaita yadda ya kamata.
Hasan ya kuma bayyana fatan da ‘yan wasan kasar sa Pakistan ke yi na zuwan wannan gasa ta hunturu, yana mai cewa sun kagu lokacin ya yi. Ya ce suna tambaya game da gasar nan ta Beijing, ina kuma bayyana musu cewa za su ji dadin kasancewar su a Sin, saboda hakan dama ce da ba za su taba mantawa da ita ba a rayuwar su.
Da ya tabo batun alaka mai zurfi dake tsakanin Sin da Pakistan kuwa, jami’in ya ce a yayin bikin bude gasar Olympic ta Beijing a shekarar 2008, kasar sa ta samu tarin wakilai a tawagar ta tamkar suna gida. Lamarin da ya samar musu da goyon baya da karfafa zuciya da jin dadi.
Hasan ya kuma yi fatan kasar sa za ta kafa fadada cudanya da Sin a fannin wasanni, kuma za ta samu tallafi daga Sin a bangaren, ciki har da gina filaye da kayayyakin bukata na wasanni, da tallafin kwarewa, matakan da a cewarsa za su taimaka wajen gina fannin wasanni, da bunkasa ci gaban rayuwar matasan Pakistan.
Hasan ya ce wasanni na da matukar tasirin hade sassan al’ummu daban daban, wanda hakan ne matakin da duniya ke bukata a yanzu haka, yayin tunkarar annobar COVID-19, kana a yi watsi da batun siyasantar da gasar Olympic.
Hasan ya ce "Ya kamata a yi amfani da wasanni wajen hade kan al’ummun duniya, wanda hakan ke kunshe da ma’anar kalmar da aka kara cikin taken gasar Olympics. Wannan shi ne abun da ya dace mu tsara...siyasantar da wannan batu ba shi da ma’ana, kuma ina da tabbacin cewa dole a yi watsi da hakan. Kaza lika a gani na gasar hunturu ta Olympics na Beijing, za a dade ba a manta da ita ba.
"Gasa ce da za ta kayatar. Za ta burge kowa. Kowa zai gamsu da ita". Ko shakka ba bu gasar Olympics ta birnin Beijing za ta aike da wani babban sako cewa, bisa hadin kai za mu iya yakar duk wata annoba ko wahalhalu ko matsaloli, har a kai ga cimma nasara ko kuma samar da damar fuskantar makoma mai kyau. Haka kuma a samu damar ba da gudummawar ci gaba da lumana a duniya baki daya.