logo

HAUSA

Babban hafsan sojin Sudan ya musanta juyin mulkin da sojoji suka yi tare da shan alwashin mika mulki ga dimokuradiyya

2021-10-27 09:27:50 CRI

Babban hafsan sojin Sudan ya musanta juyin mulkin da sojoji suka yi tare da shan alwashin mika mulki ga dimokuradiyya_fororder_211027-yaya 1

Babban kwamandan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, jiya Talata ya sha alwashin ganin an samu sauyin dimokaradiyya a kasar Sudan tare da kiyaye juyin juya halin da aka yi a watan Disamba.

Al-Burhan ya bayyana yayin wani taron manema labarai a Khartoum, babban birnin kasar cewa, "Muna son gyara turbar mika mulki, kuma abin da muka yi ba juyin mulkin soja ba ne."

Ya kara da cewa, gwamnatin da za a kafa, za ta zama gwamnatin farar hula tsantsan wadda za ta kunshi cancantar kasa kuma ba za ta hada da wani bangare ba. Yana mai cewa, za a soke dokar ta baci da aka sanya a fadin kasar, da zarar an kafa gwamnatin farar hula.

A ranar Litinin ne, Al-Burhan ya kafa dokar ta-baci a fadin kasar, tare da rusa majalisar rikon kwaryar kasar, da ma gwamnonin jihohin kasar.

Tun daga wannan lokacin ne, masu zanga-zanga suka fito kan titi a birnin Khartoum, inda suka yi watsi da matakan da Al-Burhan ya sanar, inda suka bukaci a kafa gwamnatin farar hula.

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok tare da mai dakinsa, sun koma gida karkashin tsauraran matakan tsaro, kamar yadda ofishin firaministan ya bayyana a shafinsa na Facebook jiya Talata. (Ibrahim)