logo

HAUSA

Jakadan Sin dake jamhuriyar Niger ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2021-10-27 10:21:54 CRI

Jakadan Sin dake jamhuriyar Niger ya gana da ministan harkokin wajen kasar_fororder_微信图片_20211027102129

Jiya Talata, jakadan Sin dake jamhuriyar Niger Jiang Feng ya gana da ministan harkokin wajen kasar Hassoumi Massoudou, inda suka yi musayar ra’ayi game da huldar kasashen biyu da ma hadin kansu.

Jiang Feng ya nuna cewa, huldar kasashen biyu tana bunkasa yadda ya kamata, kuma za su kira taron wakilan tattalin arziki da ciniki tsakaninsu. Ya ce, Sin na fatan za ta yi amfani da wannan zarafi mai kyau, don kara hadin kan kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare da tuntubar juna, ta yadda za a ingiza huldar hadin kansu zuwa gaba.

A nasa bangare, Hassoumi Massoudou ya jinjinawa huldar hadin kai ta sada zumunta dake tsakanin kasashen biyu. Malam Hassoumi Massoudou ya ce, ci gaban da kasashen biyu suke samu ta fuskar hadin kansu, tana amfanawa jama’arsu baki daya. Niger na fatan kara hada kai da kasar Sin don gudanar da taron da kwamitin tattalin arziki da cinikayya na hada kan bangarorin biyu zai shirya, da kuma tabbatar da ganin an aiwatar da sakamakon taron, ta yadda za a ciyar da huldar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki nan gaba. (Amina Xu)