logo

HAUSA

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2021-10-27 19:04:53 CRI

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar_fororder_jakada

Jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama a ranar Litinin. Yayin zantawar su, Mr. Cui Jianchun ya ce a bana ake cika shekaru 50, da dawowa janhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerar ta a MDD. Kuma Sin ta godewa Najeriya bisa kuri’ar amincewa da hakan da ta jefa a zauren MDD shekaru 50 da suka gabata, tana kuma fatan ci gaba da kyautata yanayin alakar ta da Najeriya.

A nasa bangare Mr. Onyeama, ya ce alakar dake tsakanin kasashen 2 tana da kyau matuka, kuma Najeriya ta ci gajiya sosai daga alakar ta da kasar Sin.  (Saminu)