logo

HAUSA

Rawar da Jamhuriyar jama’ar Sin ta taka shekaru 50 bayan dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD

2021-10-27 09:03:59 CRI

A ranar Litinin 25 ga watan Oktoban wannan shekara ce, Jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta yi bikin murnar cika shekaru 50 da dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD. A jawabin da ya gabatar yayin bikin da ya halarta a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, shekaru 50 da dawowa da jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD, shekaru 50 ne na ci gaban kasar Sin cikin lumana da kuma moriyar bil-adama.

Rawar da Jamhuriyar jama’ar Sin ta taka shekaru 50 bayan dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD_fororder_211027世界21040-hoto1

A cikin shekaru 50 din da suka gabata, jama'ar kasar Sin sun ci gaba da gudanar da ruhin kyautata kansu, da fahimtar alkiblar ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin sauyin yanayi, kuma sun rubuta tarihin kasar Sin da ci gaban da bil-adama ya samu.

Haka kuma a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, al'ummar kasar Sin a ko da yaushe suna hada kai, da yin hadin gwiwa da jama'ar kasashen duniya, da kiyaye daidaito da adalci na kasa da kasa, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.

Rawar da Jamhuriyar jama’ar Sin ta taka shekaru 50 bayan dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD_fororder_211027世界21040-hoto3

A cikin shekaru 50 da suka gabata, jama'ar kasar Sin sun kasance a ko da yaushe suna goyon bayan hukuma da matsayin MDD, suna gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, kana hadin gwiwar Sin da MDD ya kara zurfafa. Xi ya kuma sanar da jerin shawarwari da matakan da Sin za ta dauka wajen goyon bayan sha’anin MDD, ciki hadda kafa asusun tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa na Sin da MDD, asusun taimakawa hadin kan kasashe masu tasowa, kuma wannan shi ne karon farko da ta kafa kwalejin hadin kai da samun bunkasuwa tsakanin kasashe masu tasowa da sauransu.

Rawar da Jamhuriyar jama’ar Sin ta taka shekaru 50 bayan dawo mata da halastacciyar kujerarta a MDD_fororder_211027世界21040-hoto4

Kasar Sin ta gabatar da wadannan shawarwari da matakai tare da samun ci gaba mai armashi. Daga cikinsu, an mai da asusun samun zaman lafiya da bunkasuwa na Sin da MDD a matsayin mataki mai karfi wajen goyon bayan sha’anin MDD da sa kaimi ga hadin kai tsakanin bangarori daban-daban. Ya zuwa yanzu, Sin ta zuba dala miliyan 120 cikin wannan asusu, tare da aiwatar da ayyuka 112 cikin hadin kai, matakin da ya taimakawa aikin shinfida zaman lafiya da bunkasuwa da majalisar ta gudanar. A watan Satumba na shekarar 2020, Sin ta sanar da tsawaita wa’adin asusun na tsawo shekaru 5 bayan wa’adinsa ya kare a shekarar 2025. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)