logo

HAUSA

Sin na nacewa manufar kare cudanyar sassa daban daban

2021-10-27 19:00:17 CRI

Sin na nacewa manufar kare cudanyar sassa daban daban_fororder_sin

Cikin jawabin da ya gabatar, yayin bikin cika shekaru 50 da dawowa jamhuriyar jama’ar kasar Sin da halastacciyar kujerar ta a MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar kasarsa, ta kiyaye iko da matsayin MDD, tare da nacewa manufar kare cudanyar sassa daban daban.

Yayin jawabin wanda ya gabatar a ranar Litinin, shugaban na Sin ya jaddada mahangar kasarsa, game da abun da duniya ke bukata, don gane da muhimmin matsayin ta a matakin gudanar da harkokin kasa da kasa.

Ya ce cikin shekaru 50 da suka gabata, muhimmin darasi da Sin ta samu yayin cudanyar ta da MDD, shi ne nacewa bin tafarkin cudanyar sassa daban daban. Kuma a shekarun baya bayan nan, game da tambayar da a kan yi cewa, me ya sa duniya ke bukatar cudanyar sassa cikin ‘yanci, da kuma wace irin cudanya ce ake bukata, shugaba Xi ya jaddada cewa, muhimmancin cudanyar dukkanin sassa shi ne samar da damar warware  matsalolin kasa da kasa tare, yayin da kuma jimillar kasashen duniya ke iya saita makoma da alkiblar duniya cikin hadin gwiwa.

Ya ce wannan akida ce ta Sin. Wadda ke amsa tambaya game da dabarar ingiza daidaito cikin tsarin alakar kasa da kasa, wanda ke ci gaba da fuskantar sauye sauye da gyare gyare.  (Saminu)