logo

HAUSA

Sai An Zubar Da Ruwa A Kasa Kafin A Taka Damshi

2021-10-27 17:14:52 CRI

Sai An Zubar Da Ruwa A Kasa Kafin A Taka Damshi._fororder_hoto

A yau, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani mai taken "Daukar mataki kan sauyin yanayi: Manufofin kasar Sin da ayyukanta” domin adana irin ci gaban da kasar ta samu wajen dakile matsalar sauyin yanayi, da kuma raba gogewarta da hanyoyin da take bi wajen magance wannan matsala da sauran kasashen duniya.

A kwanakin baya ne, kasar Sin ta karbi bakuncin taron kare mabambantan halittu na MDD karo an 15, a wani mataki na kare halittu da ma kiyaye duniyar da bil-Adama da nau’o’in halittu ke rayuwa cikin jituwa. Wannan wani bangare ne na matakan da masana kiyaye muhalli ke kira a kowa ne lokaci, wajen ganin an kare muhallin da muke rayuwa daga gurbacewa da ma bacewar nau’o’in halittu dake taimakawa rayuwar bil-Adama ta wasu fuskoki.

Kafin wannan taro, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani, wadda ta yi fashin baki dangane da yadda kasar ta yi namijin kokari, a fannin kare nau’o’in halittu mabambanta, duk wannan a cewar masharhanta, wani mataki ne na kare duniyar da muke rayuwa.

Wannan ne dai karon farko da kasar ta fitar da irin wannan takarda, wadda ta fayyace ma’anar aikin, da manyan matakai da ake aiwatarwa, da nasarorin da kasar ta cimma, tare da gudummawar ta a fannin ga sassan kasa da kasa.

Kare nau’o’in halittu mabambanta muhimmin jigo ne na inganta rayuwar bil adama da ma ci gaban sa. Wannan ya sa kasar Sin har kullum, take dora muhimmancin gaske ga batun da ya shafi muhalli baki daya. Bayan wannan namijin kokari, sai kuma a baya-bayan mahukuntan kasar ta Sin, suka bayyana nasarorin da suka cimma a dangane da jimillar yankin da kasar ta gudanar da gine-gine wanda ya zarce murabba’in mita biliyan 6.6, a kokarin da kasar ke yi na samun bunkasuwa mai inganci a birane da kauyukan kasar.

Da yake karin haske kan nasarorin da kasar ta samu a fannin samun bunkasuwa a birane da kauyuka, mataimakin ministan kula da gidaje, raya birane da yankunan karkara na kasar Sin, Zhang Xiaohong ya jaddada wahalar da aka fuskanta a fannin tsimin makamashi da rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a birane da kauyuka.

Ma'aikatar ta bayyana kudirinta na ci gaba da yin kokarin kara yawan gine-gine marasa gurbata muhalli, da kara ingancin makamashi, da inganta gine-gine wadanda ba sa amfani da makamashi sosai a yankunan da suka dace da yanayi, da gyara gine-ginen da ake da su a halin yanzu, don kara ingancin makamashi da rage fitar da iskar Carbon. Duk wadannan matakai ne na kare muhallin duniyarmu daga gurbacewa. Sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi.

Bisa ka’idar da aka tsara, za a kafa tsarin cibiyoyi da manufofin raya birane da kauyuka ba tare da gurbata muhalli ba nan da shekarar 2025 a kasar Sin, yayin da shirin samun bunkasuwa ba tare gurbata muhalli ba, zai karade birane da kauyukan kasar baki daya nan da shekarar 2035, tare kuma da kara rage fitar da iskar Carbon. Wannan ya kara nuna yadda kasar Sin ke aiwatar da dukkan matakan da ta yi alkawarin dauka a fannin kare muhalli a zahirance maimakon maganar fatar baka. Kyan alkawari aka ce cikawa.

Da fatan ragowar kasashen duniya ma, za su yi koyi da matakan da kasar Sin take dauka wajen kare muhallin duniyarmu daga gurbata. Sanin kowa ne cewa, hannu daya ba ya daukar jinka. (Ibrahim Yaya)