logo

HAUSA

Sin Ta Samu Karbuwa A Wajen MDD Saboda Manufar Yin Watsi Da Babakere Da Wakiltar Muradun Kasashe Masu Tasowa

2021-10-26 15:51:43 CRI

Sin Ta Samu Karbuwa A Wajen MDD Saboda Manufar Yin Watsi Da Babakere Da Wakiltar Muradun Kasashe Masu Tasowa_fororder_src=http___wx2.sinaimg.cn_crop.0.54.1738.966_006N4ALSgy1gmdueoxaz9j31ca0u01kx&refer=http___wx2.sinaimg

Daga Amina Xu

Jama’a, shin ko kun san dalilan da suka sa kasashen Afrika suka goyi bayan jamhuriyyar jama’ar kasar Sin game da dawowarta cikin MDD? Ran 25 ga watan Oktoba na shekarar 1971, MDD ta zartas da kuduri mai lamba 2758 don dawowa Sin halastaciyyar kujerarta a majalisar, a yayin taron, wakilin kasar Tanzaniya a waccan lokaci Salim Ahmed Salim ya yi tsalle don farin ciki, yayin da sauran wakilan Afrika suka rika yin shewa da tafi har tsawon mintoci 2, abin da ba a taba gani ba a tarihin MDD.

Amma me ya sa Sin ta samu goyon bayan kasashen Afrika? Dalilin shi ne: Sin ba ta da niyyar yin babakere a duniya, kuma tana kokarin bunkasa dangantakarta da Afrika don amfanawa juna da cin moriya tare, kuma Sin tana wakiltar muradun kasashe maso tasowa.

Qiao Guanhua, wanda ya jagoranci tawagar wakilan kasar Sin halartar taron, ya taba bayyana a yayin taron cewa, babbar kasa mafi karfi ta kan yi babakere, amma Sin ba za ta zama irin wannan kasa ba har abada, ba za ta kai hari ko tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe ba. Yanzu, Sin ta samu ci gaba mai armashi ta hanyar dogaro da kanta da bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, amma Sin ta nace ga alkawarin da ta yi cewa, ba za ta taba yin babakere ko kai hari kan sauran kasashe ba. Saboda haka, kasashen Afrika wadanda suka sha fama da mulkin mallaka suna mutunta da goyon baya kasar Sin.

Ita ma Sin ta taba fama da mulkin mallaka, hakan ya sa ba ta so abokanta kasashen Afrika wadanda suka samu ‘yancin kai, su koma mawuyancin hali, don haka, take kokarin taimakawa kasashen Afrika yaki da mulkin mallaka da samun ‘yancin al’ummarsu. Ba ma kawai ta samar musu tallafi a fannin tattalin arziki ba, har ma ta taimakawa musu gina manyan ababen more rayuwa, alal misali, layin dogo na Tanzaniya ya zama alama na dadadden zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu! Ya zuwa yanzu, manyan ababen more rayuwa kamar wannan layin dogo da Sin ta gina ko take ginawa a Afrika, sun bayyana yadda zumuncin Sin da Afrika ya amfani juna da cin moriya tare, kuma ya zama dalilin da ya sa kasashen Afrika suke goya mata baya.

Sin ta samu bunkasuwa da wadata, daga kasa maras karfi da talauci, hakan ya sa ba za ta mantawa da matsayinta na kasa mai tasowa ba, shi ya sa take kokarin taimakawa kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa. Ko da yake an kawo karshen mulkin mallaka a duniya, amma har yanzu wasu kasashe masu tasowa na fama da tasirin da mulkin mallaka ya haifar musu. A matsayinta na wakiliyar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, Sin ta sauke nauyin dake wuyanta na tabbatar da muradu da kiyaye hakkokin kasashe masu tasowa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban magatakardan MDD António Guterres kwanan baya, inda ya shaida masa cewa, ya kamata MDD ta sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa, musamman ma tabbatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, da yarjejeniyar Paris dangane da sauyin yanani, da kuma ba da kulawa ga kasashe masu tasowa da samar musu da taimako. Kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa kasashe masu tasowa wajen ganin sun samu karbuwa da amincewa daga kasashen Afrika.

Kasar Sin kasa wadda ta yi alkawarin yin watsi da babakere da cin moriyar juna da samun nasara tare da kasashen Afrika da kuma wakiltar muradun kasashe masu tasowa, ta samu karubwa da amincewa daga kasashe mambobin MDD a shekaru 50 da suka gabata, ba shakka, wadannan kasashe za su ci gaba da mutunta da amincewa da ita. (Amina Xu)