logo

HAUSA

Yan Zimbabwe sun yi boren adawa da takunkuman da Amurka ta kakaba

2021-10-26 10:05:50 CRI

Yan Zimbabwe sun yi boren adawa da takunkuman da Amurka ta kakaba_fororder_a01-Zimbabweans march against US

A ranar Litinin al’ummar kasar Zimbabwe sun yi gangami a duk fadin kasar domin tunawa da ranar nuna adawa da takunkuman da kasar Amurka ta kakaba, inda suka nemi ta janye takunkuman da ta kakabawa kasar ta kudancin Afrika kusan shekaru 20 da suka gabata.

Ranar nuna adawa da takunkumin wanda ya samu goyon bayan kungiyar raya al’ummar kasashen shiyyar kudancin Afrika SADC domin taya kasar Zimbabwe adawa tare da yin kiraye kirayen neman janye takunkuman ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

A babban birnin kasar Harare, wasu gamayyar kungiyoyin ’yan gwagwarmaya na cikin gida wato BAAS, masu nuna adawa da takunkuman, sun gudanar da zanga zangar lumana a ofishin jakadancin Amurka inda suka bukaci ta janye takunkuman.

Calvern Chitsunge, shi ne ya jagoranci kafa gamayyar kungiyar ta BAAS, ya ce takunkuman sun yi matukar jefa rayuwar al’ummar kasar Zimbabwe cikin kunci, don haka kungiyar SADC ta shiga cikin ayarin masu neman a janye takunkuman.

Zimbabwe ta jima tana fadi tashin fama da takunman da aka kakaba mata daga bangare guda na kasashen yamma wanda Amurka ke jagoranta. (Ahmad)