logo

HAUSA

Dawowar Halaltacciyar Kujerar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin A MDD, Nasara Ce Ga Duniya Ba Kasar Kadai Ba

2021-10-26 19:51:55 CRI

Dawowar Halaltacciyar Kujerar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin A MDD, Nasara Ce Ga Duniya Ba Kasar Kadai Ba_fororder_hoto

Cikar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 50 da dawowar halaltacciyar kujerarta a MDD, babbar nasara ce ga duniya baki daya, ba kasar kadai ba. Domin adadin al’ummun duniya da suka ci gajiyar hakan, har ya fi na al’ummar kasar yawa.

Sannu sannu, kasar Sin ta zama abar koyi a duniya, ganin irin hakuri da jajircewarta da uwa uba shugabanci na gari karkashin jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin. A ganina, dawowar kujerar hannun kasar Sin, ya fi amfanawa sauran sassan duniya maimakon ita kanta kasar. Dalili shi me, irin gagarumar gudunmuwa da take bayarwa wajen kai dauki da kyautata rayuwar al’ummar duniya. Zuwa yanzu, Sin ta zama mai kujerar naki a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, haka kuma ta zama mai babbar murya da ake jin amonta a ko ina. Ta tsaya tsayin daka wajen kare muradun kasashe masu tasowa musammam kasashen Afrika. Ta kasance mai bayar da gudunmuwa ga wanzuwar zaman lafiya a duniya, bisa la’akari da adadi dakarunta  dake wanzar da zaman lafiya a dukkan sassan duniya. Haka kuma, ta kasance kasa ta biyu a duniya da ta fi bayar da gudunmuwar kudi ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar.

Baya ga haka, sanin kowa ne ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, wadda ke bada gudunmuwar kimanin kaso 17 na jimilar tattalin arzikin duniya. Haka zalika a fannin cinikayya da tsarin samar da kayayyaki cikin sauki. Ina da yakinin cewa a duk inda aka kira sunan kasar Sin a duniya, batun samar da kayayyaki daban-daban masu inganci da rahusa, shi ne abun da mutane za su yi tunani. Albarkacin kasar Sin, mutanen duniya sun samu kayayyakin da suke so. Kuma addadin mutanen da suka dogara da kansu ta hanyar sayar da kayayyakin kasar Sin, ba zai lissafu ba.

Cikin wadannan shekaru, Sin ta kasance mai kiyaye ka’idoji da dokokin Majalisar Dinkin Duniya, haka zalika mai rajin tabbatar da huldar kasa da kasa bisa girmama juna da adalci. Wannan ne ya sa kasashe masu tasowa, misali na Afrika  da suka yi fama da mulkin mallaka, yanzu suke more fasahohi na zamani da ababen more rayuwa sanadiyyar kawancesu da ita, wanda ya kai su ga samun ci gaba a fannoni da dama.

Idan muka duba bangaren ajandar ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya, kasar Sin ta yi gagarumar tasiri kan wannan ajanda, musammam a fannin yaki da talauci, a matsayinta na kasa mai tasowa, lamarin da ke nuna cewa, sauran kasashen duniya na da kyakkyawan fata na yakar talauci. Haka zalika fannin kiyaye muhalli da yaki da sauyin yanayi da yaki da annoba da sauran muhimman batutuwa da suk shafi kasa da kasa.

Hakika ya kamata al’ummu daban daban na duniya su yi murna da wannan rana ta cika shekaru 50 da dawowar kujerar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a MDD, sannan su tuna da irin rawar da Sin ke ci gaba da takawa a kokarinta na gina duniya mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama. (Fa’iza Mustapha)