logo

HAUSA

Sin ta himmatu wajen wanzar da ci gaba tana kuma maraba da dukkanin kasashen duniya su shiga a dama da su

2021-10-26 20:05:24 CRI

Sin ta himmatu wajen wanzar da ci gaba tana kuma maraba da dukkanin kasashen duniya su shiga a dama da su_fororder_sin

Cikin jawabin da ya gabatar, yayin bikin cika shekaru 50 da dawowa jamhuriyar jama’ar kasar Sin da halastacciyar kujerar ta a MDD, shugaban Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa ta himmatu wajen wanzar da ci gaba, tana kuma maraba da dukkanin kasashen duniya da su zo a yi wannan tafiya tare. Ya kuma tabo misalin irin nasarorin da aka cimma a fannin samar da manyan ababen more rayuwa, kuma daga layin dogo na Tanzania zuwa Zambia, zuwa shawarar ziri daya da hanya daya, da tallafin da kasar ke baiwa kasashe masu tasowa, da samar da damammaki ga kasashen duniya daga ci gaban kasar ta Sin.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, Sin za ta nacewa hanyar aiwatar da sauye sauye da bude kofa ga waje, za ta kuma ci gaba da ba da gudummawa ga ci gaban duniya. Tana kuma gabatar da shawarar shigar kasashen duniya, cikin manufar nan ta hadin gwiwar tattalin arziki da zamantakewar sassa daban daban, don amfanar daukacin al’ummar duniya. (Saminu)