logo

HAUSA

AU ta yi kira a gaggauta tuntubar juna game da batun Sudan

2021-10-26 13:51:45 CRI

AU ta yi kira a gaggauta tuntubar juna game da batun Sudan_fororder_a04-AU calls for immediate consultations in Sudan

Shugaban kungiyar tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, ya yi kiran a gaggauta tuntuba kan batun kasar Sudan.

Jagoran kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55, ya sake yin kiran a gaggauta dawowa kan teburin tuntubar juna tsakanin bangaren fararen hula da bangarorin sojojin kasar ta Sudan karkashin dokokin siyasa da aka ayyana da kuma dokar kundin tsarin mulkin kasar.

Tun da farko a ranar Litinin, shugaban majalisar mulkin sojoji na kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar ta Sudan, kana ya rusa gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Matakin ya zo ne ’yan sa’o’i kadan bayan kame firaministan gwamnatin rikon kwarya bangaren fararen hular kasar Sudan, Abdallah Hamdok, da ministocin da dama wadanda gamayyar dakarun sojojin kasar suke tsare da su. (Ahmad Fagam)