logo

HAUSA

Najeriya ta fara amfani da kudin Intanet na farko da babban bankin kasar ya kirkiro

2021-10-26 09:39:55 CRI

Najeriya ta fara amfani da kudin Intanet na farko da babban bankin kasar ya kirkiro_fororder_211026-Ibrahim1-eNaira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a jiya Litinin ya kaddamar da eNaira, kudin Intanet na farko da babban bankin kasar CBDC ya kirkiro, inda ta zama kasa ta farko a Afirka wadda ta fara amfani da kudin Intanet a hukumance.

Yayin da yake kaddamar da eNaira a Abuja, babban birnin kasar, shugaba Buhari ya lura cewa, Najeriya tana daya daga cikin kasashen da suka fara gabatar da kudin na Intanet ga ’yan kasarta.

Shugaba Buhari ya bayyana yayin kaddamar da eNairan a fadar gwamnati dake Abuja cewa, abin da yake faruwa a ’yan shekarun baya-bayan nan a duniya, shi ne yadda ake samun raguwar amfani da tsabar kudi a zahiri wajen gudanar da harkokin kasuwanci.

Ya kara da cewa, galibin manyan bankunan duniya, sun fara tunanin gabatar da kudaden Intanet don gudanar da harkokin kasuwanci da sayan kayayyakin bukatu na gida cikin sauri, da aminci, cikin sauki, da kuma arha, a matsayin martani ga abubuwan da aka ambata a baya

Ya kara da cewa, wasu kasashe da suka hada da Sin, da Bahamas, da Cambodia sun riga sun gabatar da kudadensu na Intanet. Yana mai cewa, amincewa da kudin na Intanet da fasaharsa da ake kira Blockchain, na iya kara yawan kayayyakin cikin gidan Najeriya ya zuwa dalar Amurka biliyan 29 nan da shekaru 10 masu zuwa. (Ibrahim)