logo

HAUSA

Sin ta kafa tarihin ba da gudummawa ga zaman lafiyar duniya

2021-10-25 21:16:21 CRI

Sin ta kafa tarihin ba da gudummawa ga zaman lafiyar duniya_fororder_sin

A yau Litinin 25 ga watan Oktoba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin cika shekaru 50, tun bayan dawowa janhuriyar al’ummar kasar Sin da halastacciyar kujerar ta a MDD, inda ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da nacewa hanyar samar da ci gaba, tare da ba da gudummawar gina zaman lafiya a duniya.

Kaza lika a wannan rana, shi ma babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya godewa kasar Sin, bisa muhimmiyar rawa da take takawa wajen tallafawa zaman lafiya da ci gaban duniya.

A kan yi tambayar dalilin da ya sanya har kullum Sin ke zama jigon gina zaman lafiyar duniya. Dalilin kuwa shi ne, zaman lafiya wani gado ne cikin al’adun al’ummar Sin cikin sama da shekaru 5,000 da suka gabata, kana yana cikin tsatson JKS. Don haka, Sin ta sha nanata cewa, duk irin ci gaban da ta samu, ba za ta taba amincewa da babakere, ko manufar mamayar wasu sassa na daban ba.  (Saminu)