logo

HAUSA

Majalissar koli a Sudan ta ayyana dokar ta baci bayan da aka tsare firaministan kasar

2021-10-25 19:29:22 CRI

Jagoran majalissar kolin kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya ayyana dokar ta baci a dukkanin sassan kasar a yau Litinin, bayan da wasu sojoji suka damke firaminista Abdalla Hamdok.

Baya ga firaministan, rahotanni sun tabbatar da cewa an yi awon gaba, da wasu fararen hula mambobin majalissar zartaswar rikon kwaryar kasar, da wasu ministocin kasar.  (Saminu)