logo

HAUSA

Alluran riga kafin COVID-19 na kasar Sin sun bunkasa aikin riga kafin Habasha

2021-10-25 10:14:57 CRI

Alluran riga kafin COVID-19 na kasar Sin sun bunkasa aikin riga kafin Habasha_fororder_211025-yaya 2-Habasha

A jiya ne, rukunin baya-bayan na allurar rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm da yawansu ya kai 800,000 da kasar Sin ta bayar da gudummawa, ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, lamarin da ya habaka aikin riga kafin kasar dake gabashin Afirka.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta ba da gudummawar alluran rigakafin COVID-19 sama da miliyan 1.8 ga Habasha, wanda gwamnatin Habasha ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen yakar cutar.

A zantawarta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiyan, ministar lafiya ta kasar Habasha Lia Tadesse ta ce, allurar rigakafin da kasar Sin ta ba da taimako, ta yi tasiri sosai yayin da bayanai ke nuna cewa, mutanen da aka yi wa allurar ba su da saurin hadarin kamuwa da cutar ta COVID-19 fiye da wadanda ba a yi musu allurar ba.

Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar na nuna cewa, ya zuwa yanzu, Habasha ta yi alluran rigakafi 4,286,768 ga mutane 3,211,211

Allurar rigakafin da kasar Sin ta bayar, a matsayin daya daga cikin allurar rigakafin COVID-19 da ake yi a kasar, suna kara samun karbuwa a tsakanin ’yan kasar

A matsayin wani bangare na kudurin da ta dauka na mayar da allurar rigakafinta a matsayin hajar amfanin jama'a a duniya baki daya, a halin yanzu kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da allurar riga-kafin cikin sauki da araha a kasashe masu tasowa ciki har da Habasha.

Kasar Sin za ta yi kokarin samar da alluran rigakafin COVID-19 biliyan 2 ga duniya a cikin wannan shekara tare da ba da dalar Amurka miliyan 100 ga shirin COVAX, inda za a yi amfani da wadannan kudade wajen rarraba alluran rigakafin ga kasashe masu tasowa. (Ibrahim Yaya)