logo

HAUSA

Yan sandan Uganda sun bayyana fashewar bam a babban birnin kasar a matsayin aikin ta’addanci na cikin gida

2021-10-25 10:35:45 CRI

Yan sandan Uganda sun bayyana fashewar bam a babban birnin kasar a matsayin aikin ta’addanci na cikin gida_fororder_211025-Ahmad 2-Uganda

Hukumar ’yan sandan kasar Uganda ta bayyana fashewar bam da ya faru a daren Asabar a babban birnin kasar Kampala a matsayin ta’addancin cikin gida.

Fred Enanga, kakakin hukumar ’yan sandan kasar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, wasu mutane uku ne suka yi badda kama a matsayin kwastomomi a kantin sayar da abinci dake Komamboga, a birnin Kampala, inda suka tada abubuwan fashewa bayan sun bar wajen.

Enanga ya bayyana cewa, har yanzu ba a gano manufar ’yan ta’addan ba.

Yan sandan sun sauya alkaluman adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata, sun bayyana cewa, mutum guda ne ya mutu sannan mutane uku sun samu munanan raunuka. Da farko ’yan sandan sun bada rahoton mutuwar mutane biyu da kuma jikkatar mutane bakwai.

Tun da farko da safiyar ranar Lahadi, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya ce za a damke mutanen dake da hannu wajen kitsa harin.

Harin bam din na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ofisoshin jakadancin Birtaniya da Faransa sun baiwa ’yan kasashensu gargadi, game da yiwuwar harin ta’addanci. (Ahmad)