Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin Na Shan Yabo Bisa Jajurcewarta
2021-10-25 19:39:46 CRI
Yayin da a yau 25 ga watan Oktoba, ake bikin cika shekaru 50 da dawowar halastacciyar kujerar wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD, shugabannin kasashen duniya da jami’an diflomasiyya gami da shugabannin kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa na cigaba da yin tsokaci da yin Allah sam barka bisa ga irin nasarorin da kasar ta cimma da kuma gagarumar gudunmawar da ta samarwa duniya a dukkan fannoni.
Yayin ganawarsa ta kafar bidiyo a yau 25 ga watan Oktoba, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce, yau shekaru 50 da suka gabata, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta samu dawowar wakilcinta a MDD. Wannan wata muhimmiyar rana ce, kuma ina taya murnar wannan rana. Guterres ya ce ci gaban kasar Sin ya samar da damammaki ga duniya. Muna godiya ga kasar Sin bisa yadda ta jajurce wajen kiyaye huldar bangarori daban daban, taimakon da take bayarwa ga ayyukan MDD da kuma muhimmiyar rawar da take takawa da gudunmawarta ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa da kasa. Hakika MDD tana matukar nuna godiya ga kasar Sin bisa rawar da ta taka wajen kawar da talauci, da jure matsalolin sauyin yanayin duniya, da kiyaye mabanbantan halittu, da daga matsayin aikin samar da riga-kafin cutar Covid-19. A nasa bangaren, Abdullah Shahid, wanda shi ne shugaban babban taron MDD (UNGA) karo na 76, ya taya jamhuriyar jama’ar kasar Sin murna game da gagarumar gudunmawar da ta baiwa duniya tun bayan maido mata da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD. Ya ce Sin ta taka rawar gani a hadin gwiwar bangarori daban daban, domin kuwa a halin yanzu kasa ce ta biyu a duniya mafi bayar da gudunmawa na kasafin kudin ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD. Sannan tana jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya kimanin 29, bugu da kari ta bayar da gudunmawar dakarun aikin wanzar da zaman lafiya sama da 50,000. Shahid ya ce, yana matukar farin ciki da jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping da ya gabatar a taron mahawara karo na 76 na babban taron MDD, wanda ya tabo batun cewa kasar Sin za ta kara fadada tallafinta zuwa ga sauran kasashe masu tasowa domin bunkasa samar da makamashi mai tsafta wanda ba zai gurbata muhalli ba. Game da annobar COVID-19, kasar Sin ta taka rawar gani inda ta lashi takobin samar da alluran riga-kafin COVID-19 biliyan 2 ga duniya nan da karshen wannan shekara. Shi ma tsohon jami’in diflomasiyyar kasar Zambiya ya bayyana cewa, maido da halaltacciyar kujerar wakilcin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a MDD a shekarar 1971 ya kasance daya daga cikin manyan nasarorin da ya samu a lokacin da yake kan ganiyar aikinsa. Vernon Mwaanga, tsohon wakilin kasar Zambiya a MDD, ya ce babu tantama, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a tsarin ayyukan MDD a shekaru 50 da suka gabata a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Ya kuma yi waiwaye game da yadda kasashen Afrika suka goyi bayan jamhuriyar jama’ar kasar Sin don maido da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD. Ya ce, wakilan kasashen Afrika sun yi matukar nuna jajurcewarsu tare da yin amanna cewa ba zasu taba lamintar yankin Taiwan, wanda bangare ne na kasar Sin, ya zama shi ne ke wakiltar kasar Sin ba. Ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Afika tana da kyakkyawar makoma, duba da yadda ake kara samun gagarumin ci gaban hulda a tsakanin bangarorin, kana dangantakar bangarorin biyu ta kara karfafa ta hanyar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, da shawarar “ziri daya da hanya daya. (Ahmad Fagam)