logo

HAUSA

Tsohon jami’in diflomasiyyar Zambia ya bayyana maido da halaltacciyar kujerar wakilcin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a MDD

2021-10-24 21:11:47 CRI

Tsohon jami’in diflomasiyyar Zambia ya bayyana maido da halaltacciyar kujerar wakilcin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a MDD_fororder_211024-Ahmad5-Zambia

Wani tsohon jami’in diflomasiyyar kasar Zambiya ya bayyana cewa, maido da halaltacciyar kujerar wakilcin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a MDD a shekarar 1971 ya kasance daya daga cikin manyan nasarorin da ya samu a lokacin da yake kan ganiyar aikinsa.

A yayin tattaunawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, gabanin bikin cika shekaru 50 da cimma wannan gagarumar nasara, wanda ya fado a ranar 25 ga watan Oktoba, Vernon Mwaanga, tsohon wakilin kasar Zambiya a MDD tsakanin shekarun 1968 zuwa 1972, ya yi waiwaye game da yadda kasashen Afrika suka goyi bayan jamhuriyar jama’ar kasar Sin don maido da halaltaciyyar kujerar wakilcinta a MDD.

Mwaanga ya ce, wakilan kasashen Afrika sun yi matukar nuna kaunarsu na samar da sauyi saboda sun yi amanna cewa ba zai taba yiwuwa yankin Taiwan, wanda bangare ne na kasar Sin, ya zama ya wakilci kasar Sin ba.

“Za ka iya yin tunani game da irin matsin lambar da muka fuskanta, saboda mun dauki nauyin samar da kudirin doka a shekarun 1966, 1967, 1968, 1969, 1970 daga karshe mun yi nasara a shekarar 1971," in ji Mwaanga.

Zambia tana daya daga cikin kasashen Afirka 23 wadanda suka rattaba hannu don gabatar da kudirin nuna goyon bayan maido da halastacciyar kujerar wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD.

Mwaanga ya ce, domin dacewa da tsarin MDD, gamayyar kasashen Afrika sun nemi goyon baya daga sauran kasashen duniya inda suka bukaci su amince da kudirin, yayin da ake bukatar amincewar biyu bisa uku na wakilan kasashen kafin kudirin ya zama doka.

“A lokacin da muka kammala jefa kuri’a, har lokaci ya kure an kai dare, yayin da aka sanar da sakamakon, dukkanmu mun yi murna sosai," in ji shi.

Mwaanga, wanda aka amince ya yi jawabi a madadin gamayyar kasashen Afrika don yin maraba da sake maido wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a babban taron MDD a ranar 15 ga watan Nuwamban 1971, ya bayyana cewa, yanayi ne mai cike da matukar farin ciki mai dunbun tarihi.

Ya jaddada cewa, babu tantanma, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a tsarin ayyukan MDD a shekaru 50 da suka gabata a fannin tabbatar da zaman lafiya tsaron kasa da kasa.

Mwaanga, wanda kuma shi ne tsohon ministan harkokin wajen kasar Zambia, ya bayyana cewa, Zambia a koda yaushe tana nuna godiya ga kasar Sin bisa kudaden da ta samar tare da aikin gina layin dogo na Tanzania-Zambia saboda sauran kasashe da dama sun gaza bayar da taimako.

Ya yi amanna cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Afika tana da kyakkyawar makoma, saboda yadda ake samun gagarumin ci gaban huldar dake tsakanin bangarorin biyu wacce ta kara karfafa ta hanyar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika da shawarar “ziri daya da hanya daya, wanda kasashen Afrika suka yi lale marhabun da dukkan shawarwarin. (Ahmad Fagam)