logo

HAUSA

Sama da fursunoni 800 sun tsere sakamakon harin yan bindiga a kudancin Najeriya

2021-10-24 15:57:18 CRI

Sama da fursunoni 800 sun tsere sakamakon harin yan bindiga a kudancin Najeriya_fororder_211024-Ahmad2-Nigeria

Hukumomi a Najeriya sun ce sama da fursunoni 800 ne suka tsere bayan wani hari da ’yan bindiga suka kaddamar a gidan gyaran hali da ake tsare da su a jahar Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya, kamar yadda hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa ta tabbatar da hakan.

Olanrewaju Anjorin, kakakin hukumar gidan gyaran hali ta kasa reshen jahar Oyo, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kimanin mutane 837 dake dakon shara’a ne suka tsere daga cibiyar gyaran halin dake yankin Abolongo a jahar, bayan wani harin da ’yan bindiga suka kaddamar kan cibiyar a daren Juma’a, sai dai ba a lalata dakuna 64 dake gidan yarin ba.

Anjorin ya ce, mutane 262 daga cikin fursunonin da suka tsere din an sake damke su, inda ake ci gaba da neman 575. (Ahmad)