logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kusa miliyan 8.46

2021-10-24 15:59:34 CRI

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 8,455,978, ya zuwa yammacin ranar Juma’a.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta ce adadin mutanen da annobar ta kashe a fadin nahiyar ya kai 216,517.(Ahmad)