logo

HAUSA

Babban jami’in MDD ya yaba nasarorin da Sin ta samu a yaki da talauci

2021-10-24 15:56:27 CRI

Babban jami’in MDD ya yaba nasarorin da Sin ta samu a yaki da talauci_fororder_211024-Ahmad1-Antonio Guterres

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yaba nasarorin da kasar Sin ta cimma a yaki da fatara da sauran fannoni, inda ya bukaci kasa da kasa da su hada kai wajen magance kalubalolin dake addabar duniya.

Mista Guterres ya ce, nasarorin da kasar Sin ta cimma sun kasance a matsayin wasu muhimman darrusa ga fannin yaki da talauci wanda ya kamata a yi musayarsu a tsakanin kasashen duniya ta hanyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Babban sakataren ya kuma bayyana cewa, har yanzu duniya tana fuskantar manyan kalubaloli kamar matsalar karuwar gibin dake tsakanin masu sukuni da matalauta. Da matsolin sauyin yanayi. Da annobar COVID-19. Da rikicin siyasar kasa da kasa. Da karuwar tashen tashen hankula, da kuma yadda hakkokin dan adam ke fuskantar barazana da dai sauransu. (Ahmad)