logo

HAUSA

Yunkurin Amurka na tada rikici ta hanyar amfani da batun kare hakkin dan Adam ba zai cimma nasara ba

2021-10-23 16:50:53 CRI

Yunkurin Amurka na tada rikici ta hanyar amfani da batun kare hakkin dan Adam ba zai cimma nasara ba_fororder_Amurka-1

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gabatar da wata sanarwa a ranar 21 ga wata, inda ta zargi Sin da keta hakki da ‘yancin dan Adam a yankin Hong Kong, da kuma kin amincewa da dokar tabbatar da tsaron kasa a yankin, tana mai bukatar Sin din da ta saki masu zanga-zangar kin kasar da suka tada rikice-rikice a yankin Hong Kong da take tsare da su.

Wadannan zarge-zarge da Amurka ta yi ba su da tushe, kuma suna kara bayyana cewa, Amurkar ta yi amfani da ma’auni biyu, ta tada rikice-rikice a yankin Hong Kong.

A yayin taron kwamiti na uku na babban taron MDD karo na 76 da aka gudanar a ranar 21 ga wannan watan, wakilan kasashe fiye da 60 sun yi jawabi cikin hadin gwiwa, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Sin kan aiwatar da manufar “kasa daya mai tsari biyu”, da kin amincewa da siyasantar da batun hakkin dan Adam da amfani da ma’auni biyu kan harkokin kasa da kasa.

Wasu mutanen Amurka ba sa maida hankali kan yadda za a cimma samun zaman lafiya da tsaro mai dorewa a yankin Hong Kong, inda suke son amfani da wasu masu kin Sin da Hong Kong, wajen ci gaba da tada rikice-rikice, da kawo illa ga zaman lafiyar yankin Hong Kong, da kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Yunkurin Amurka dai, na tada rikici ta hanyar amfani da kare hakkin dan Adam ba zai cimma nasara ba. (Zainab)