logo

HAUSA

FOCAC ya karfafa yarda da inganta alakar al’ummu in ji wani masanin Afirka ta kudu

2021-10-22 10:52:35 cri

FOCAC ya karfafa yarda da inganta alakar al’ummu in ji wani masanin Afirka ta kudu_fororder_f636afc379310a551b0eaed3ba4543a9822610ea

Daraktan cibiyar nazarin al’amuran da suka shafi Sin da Afirka a jami’ar Johannesburg dake Afirka ta kudu David Monyae, ya ce dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, ya samar da wata dama ta fadada cinikayya da zuba jari, tare da inganta amincewa, da cudanyar al’ummu mabanbanta na Sin da Afirka.

David Monyae ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin wani taro ta yanar gizo game da dandalin na FOCAC, wanda cibiyar manazarta harkokin zamantakewar al’umma ta Afirka ta kudu, da hadin gwiwar wasu hukumomin bincike, da suka hada da hukumar bunkasa ci gaba ta kungiyar AU, da kungiyar hadin gwiwa don ci gaban Afirka ta AUDA-NEPAD suka kira.

Mr. Monyae ya kara da cewa, dandalin FOCAC ya zamo wani muhimmin ginshiki na kasa da kasa, wanda ke samar da zarafin kara kyautata alakar Sin da kasashen Afirka, a fannonin tattalin arziki da zamantakewa.  (Saminu)