logo

HAUSA

An saki dalibai 30 da aka sace a arewa maso yammacin Nijeriya

2021-10-22 10:09:46 CRI

Gwamnatin jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce an saki yara dalibai 30 da aka sace daga wata makarantar sakandare, sama da watanni 4 da suka gabata.

Cikin wata sanarwa, gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da sakin dalibai 30 na kwalejin gwamnatin tarayya ta yankin Birnin Yauri, tana mai cewa, sun isa Birnin Kebbi, babban birnin jihar, inda za a duba lafiyarsu kafin a sada su da iyayensu.

Sanarwar ta ruwaito cewa, ana ci gaba da kokarin ceto ragowar daliban, sai dai ba ta bayyana adadinsu ba.

Baya ga haka, gwamnatin ta bayyana godiyarta ga dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin an saki daliban. (Fa’iza Mustapha)