logo

HAUSA

Sharhi:Karya fure take ba ta ‘ya’ya

2021-10-22 12:53:54 CRI

Sharhi:Karya fure take ba ta ‘ya’ya_fororder_5bafa40f4bfbfbedc2f232006bb2b13faec31ff4

Jama’a, ko kun sha karanta rahotanni da ke cewa, wai “Jarin da kasar Sin ke zubawa Nijeriya suna haifar da matsalar bashi a kasar”, ko “Hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka sabon salon mulkin mallaka ne da kasar Sin ta aiwatar a Afirka”, ko “Bunkasuwar kasar Sin barazana ce ga duniya”? Bayan kun karanta, ko ku ma kuna kallon kasar Sin a matsayin mummunar kasa, har ma kuna fara nuna shakku kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka? Idan abin hakan yake, lallai, ya kamata ku lura, sabo da rahotannin za su iya zama na jabu, wadanda ake samarwa domin cin kudi. A watan da ya wuce, an tona asirin irin wadannan rahotannin a kasar Zimbabwe.

Bisa rahoton da jaridar The Herald ta kasar Zimbabwe ta fitar, an ce, Amurka ta yi amfani da ofishin jakadancinta dake kasar, wajen samar da kudade ga wasu cibiyoyi, domin su tsara tarukan karawa juna sani da sauran dabaru, da saye rahotannin kafafen watsa labarai masu zaman kan su, kan kudi har dalar Amurka 1000 kan ko wacce makala, inda ake umartar su da su yi rubutun suka, game da jarin da kamfanonin Sin ke zubawa a Zimbabwe. Rahoton ya ce, ban da Amurka, wasu kasashen Turai ma suna gudanar da irin wadannan ayyuka.

Bayan da aka samar da rahoton, bangarori daban daban na kasar Zimbabwe sun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da Amurka din ta tafka.

Mataimakin shugaban kasar wanda kuma shi ne ministan lafiya, Mr.Constantino Chiwenga ya ce, tun bayan bullar cutar Covid-19 a kasar Zimbabwe, kasar Sin ta samar mata babbar gudummawa ta fannonin fasaha da ma kayayyaki, matakin da ya sa Zimbabwe ta yi wa al’ummar kasar sama da su miliyan 3 rigakafi a kalla sau daya kowanensu, kuma kasar ta zama ta bakwai a fadin nahiyar Afirka wajen yawan yi wa al’ummarta rigakafin, kwatankwacin yadda wasu kasashe masu ci gaba suka yi ta tara rigakafi fiye da bukatunsu, duk da rashin daidaiton raba rigakafi da ake fuskanta a kasashen duniya daban daban.

Mr. Chiwenga ya kuma jaddada cewa, Zimbabwe ba za ta manta da gudummawar da kasar Sin ta ba ta a lokacin da take cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki, sakamakon takunkumin da kasashen yammaci suka kakaba mata.

Jaridar “The Herald” ma ya wallafa sharhi mai taken “Kada Mu Zama Daran Amurka Na Kin Jinin Kasar Sin”, wanda ya yi nuni da cewa, adalci ba shi da farashin sayarwa, ya kamata al’ummar Zimbabwe su yi hankali, don kada su zama daran da Amurka ke amfani da shi wajen nuna kin jinin kasar Sin.

Rashin kunya ne yadda Amurka ta dauki irin mataki, amma kuma ya kamata mu lura da manufar da take neman cimmawa. 

A cikin ‘yan shekarun baya, a yayin da kasar Sin ke bunkasa cikin sauri, Amurka ta fara daukarta a matsayin barazana, don haka ta yi iyakacin kokarin dakile ta. Rahotannin da ofishin jakadancinta da ke Zimbabwe ya saya a wannan karo, a hakika wani bangare ne na matakan da gwamnatin kasar ta dauka a fadin duniya don neman dakile ci gaban kasar Sin. A sa’i daya kuma, takunkumin da Amurka da ma sauran wasu kasashen yammaci suka kakaba wa Zimbabwe, bai kai ga hambarar da gwamnatin kasar ba, a maimakon haka, kasar Zimbabwe ta maido da tattalin arzikin kasar kan hanyar da ya kamata, abin da ya bakanta ran wasu ‘yan siyasar Amurka, don haka suke daukar hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Zimbabwe da ma sauran kasashen Afirka baki daya a matsayin “matsala”.

A nahiyar Afirka, dala 1000 zai iya zama taimako ga wani dalibi da ke fama da talauci, haka kuma zai iya sayen alluran rigakafin cutar Covid-19 100, sai dai abin takaici ne yadda gwamnatin Amurka ta yi amfani da kudin wajen sayen rahotanni na jabu.

Idan kuma an kwatanta kasar Sin, bisa ga dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ma shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, ya yi ta ingantawa, tare da samar da gaggaruman nasarori. In mun dauki misali da Nijeriya, da layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, da ma tashar filin jirgin sama ba Abuja, da kuma tashar jiragen ruwa na Lekki, jerin ayyukan more rayuwa ne da aka gina a kasar sun daidaita matsalolin da ke yi wa ci gaban tattalin arzikin kasar tarnaki, tare da kyautata rayuwar al’ummar kasar.

Bana ake cika shekaru 21 da kafuwar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kuma nan ba da jimawa ba za a gudanar da taron ministoci karo na takwas, na dandalin a kasar Senegal, wanda tabbas zai kara inganta hadin gwiwar sassan biyu, tare da haifar da karin alfanu ga al’ummarsu.

Jama’a, ku yi hankali a lokacin karanta rahotannin da ke shafa wa kasar Sin bakin fenti, sabo da ta yiwu akwai ciniki kan kudi har dala 1000 a bayansu. Ban da haka, za mu so mu shawarci Amurka da ta maida hankali wajen gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su amfani kasashen Afirka, maimakon furta kalamai marasa ma’ana da karairayi, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen farfadowa, da bunkasa tattalin arzikin Afirka. (Lubabatu Lei)