logo

HAUSA

Yakin Cacar Baka Ba Zai Taba Haifar Da Da Mai Ido Ba

2021-10-21 16:49:14 CRI

Yakin Cacar Baka Ba Zai Taba Haifar Da Da Mai Ido Ba_fororder_1021-01

Har kullum masharhanta na jaddada muhimmancin hadin kan sassan kasa da kasa, a fannin kawar da matsaloli da shingaye dake haddasa rashin fahimtar juna, game da batutuwan da suke shafar kasa da kasa da shiyya shiyya. Kaza lika masu bibiyar tarihi sun tabbatar da cewa, yayata kiyayya ko kyama, ko shirya karairayi, da kafa wani yanayi na salon cacar baka tsakanin kasashen duniya, bai taba haifar da wani alheri ga duniya ba.

A baya can, Amurka ta fafata yakin cacar baka da tsohuwar tarayyar Soviet, lamarin da ya haifar da daukar matakan shafawa juna bakin fenti, da kitsa makirci, da yada kiyayya tsakanin sassan biyu, kuma bayan dukkanin wadannan matakai, a karshe dai ala tilas kasashen biyu suka amince da watsi da cacar baka, suka koma teburin shawarwari domin ci gaba da warware dukkanin sabani da ka bijiro tsakanin su.

To sai dai kuma a wani yanayi mai kama da yin watsi da darasi, a baya bayan nan Amurka ta sake daura wani yakin na cacar baka, inda ta dage wajen bata sunan kasar Sin ta fuskoki da dama. Alal misali, a baya bayan nan wasu jami’an Amurka ciki har da sakataren tsaron kasar Lloyd Austin, sun zargi kasar Sin, da gina wani tsarin zamanantar da ayyukan rundunar sojin ta, wanda hakan a cewar su zai kai ga haifar da barazana, da zaman dar dar a yankin da take, tare da bunkasa takara a fannin samar da makamai.

Hakika irin wadannan kalamai na jami’an Amurka, ba komai ba ne illa yunkurin kawar da hankalin al’ummar duniya daga gaskiya. Musamman duba da cewa Amurka ita ce ma kasa mafi aiwatar da matakan bunkasa makaman kare dangi a duniya, ta kuma kafa hadin gwiwa da kawance kawayenta a fannin tsaro, tare da shiga yake yake daban daban, wadanda suka haifarwa kasashe da dama, da al’ummun su manyan bala’u, da rashin zaman lafiya da daidaito. Har ila yau, Amurka ta sha yin watsi da yarjejeniyoyin kasa da kasa masu nasaba da takaita mallakar manyan makaman yaki.

A hannu guda kuwa, mahukuntan Sin sun sha nanata matsayar su, cewa Sin ba ta da wani buri na yin takarar mallakar makamai da wata kasa, kuma tana karfafa rundunoninta na tsaro ne kawai dokin kare kai, ba wai barazana ko tsokana ba. Don haka dai fatan Sin har kullum shi ne, Amurka ta yi watsi da cacar baka, kuma a duk lokacin da ake da wani sabani, to a warware shi ta hanyar shawarwari, matakin da shi ne mafi alfanu ga sassan biyu, da ma sauran sassan duniya baki daya. (Saminu Alhassan)