logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane 343 a rubu’in uku a jihar Kadunan Najeriya

2021-10-21 09:52:50 CRI

Jimillar mutane 343 aka hallaka tare da yin garkuwa da wasu mutanen 830 a rubu’i na uku na shekarar 2021 a hare haren da ‘yan bindiga suka kaddamar a jihar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’in jihar ya bayyana.

Da yake gabatar da rahoton tsaro na watani uku uku, Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ya bayyana cewa, mutane 220 aka raunata, kana kimanin ‘yan bindiga 69 aka kashe wadanda ke kashewa ko kuma yin garkuwa da fararen hula tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.

Aruwan ya ce, an yi nasarar kubutar da mutane 101 tsakanin wannan wa’adin.

A cewar kwamishinan, ayyukan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa na karuwa ne sakamakon yadda suke samun makudan kudade, lamarin da ya kara musu kwarin gwiwar aikata mummunar sana’ar.(Ahmad)