logo

HAUSA

Dukkan mutane 21 dake cikin jirgin da ya yi hadari a Amurka sun tsira da rayukansu

2021-10-20 09:53:38 CRI

Dukkan mutane 21 dake cikin jirgin da ya yi hadari a Amurka sun tsira da rayukansu_fororder_bb31-309c907b145ee37c1be33314a9a25802

Mutane biyu sun jikkata, amma dukkan mutane 21 dake cikin jirgin da ya yi hatsari jiya Talata a gundumar Waller ta jihar Texas, sun tsira da ransu.

A cewar hukumar kula da sufuirin jiragen sama ta kasar, jirgin da ya nufi Boston, ya kama da wuta ne bayan ya ratsa shingen dake filin jirgin saman Houston, a yayin da yake kokarin tashi jim kadan bayan karfe 10 na safiya agogon wurin.

Rahotanni sun ruwaito cewa, sai da masu aikin ceto suka yi aiki na sama da awa guda a kokarinsu na kashe gobarar.

Kamfanin samar da makamashi na CenterPoint Energy, ya ce jirgin ya buge wani turken wayar lantarki a lokacin da yake tashi, lamarin da ya haifar da rashin lantarki ga kwastomominsa kusan 1,800 dake kusa da inda jirgin ya yi hatsari.

Ba a kai ga tantance ko buge turken lantarkin ne ya haddasa hatsarin ba, amma hukumar kula da sufuri ta kasar na gudanar da bincike. (Fa’iza Mustapha)