logo

HAUSA

Yara 3 sun mutu yayin da wasu mutane 10 suka jikkata sanadiyyar wani harin sama a Habasha

2021-10-20 10:35:38 CRI

Yara 3 sun mutu yayin da wasu mutane 10 suka jikkata sanadiyyar wani harin sama a Habasha_fororder_v2-0120c6a4c2325ea20f6b88c1fce60a35_1440w

Ana zaman zullumi a yankin Mekelle na Habasha, bayan wasu hare-hare ta sama biyu sun yi sanadin mutuwar yara 2 tare da jikkata wasu mutane 10.

Farhan Haq, mataimakin kakakin Sakatare Janar na MDD, ya ce ma’aikatan lafiya a yankin sun ruwaito cewa, yara 3 sun mutu yayin da wani mutum guda ya ji rauni, sanadiyyar wani hari ta sama a wajen garin Mekelle a jiya Litinin.

Kakakin ya bayyana yayin taron manema labarai na jiya cewa, hari na biyu da aka kai daga baya a jiyan, a cikin garin Mekelle, ya raunata wasu mutane 9 tare da lalata gidaje da wani otel.

Farhan Haq ya kara da cewa, tsanantar rikici abun damuwa ne, kuma MDD na tunatar da dukkan bangarori hakkin dake wuyansu karkashin dokar kasa da kasa, na kare fararen hula da kadarorinsu. (Fa’iza Mustapha)