logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga sama da 50 a arewa maso yammacin kasar

2021-10-20 10:21:36 CRI

Sama da ’yan bindiga 50 aka kashe a hare-haren da sojojin Najeriya suka kaddamar a jahar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar a ranar Litinin, kamar yadda wani jami’i ya bayyana.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da al’amurran cikin gida na jahar Kaduna, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, bayanan da rundunar sojojin ta sanar da gwamnatin jahar ya nuna cewa, dakarun tsaron suna samun gagarumar nasara, sojojin sun kashe ’yan bindiga sama da 50, wadanda aka fi sani da ’yan fashin daji, a lugudan wuta da sojojin suka kaddamar ta sama da ta kasa a yankin karamar hukumar Birnin Gwari dake jahar.

Aruwan ya ce, hare-haren hadin gwiwar da jiragen sojojin saman Najeriya da na kasa suka kaddamar ya yi nasarar hallaka gungun ’yan bindigar sannan ya dakile wani yunkurin harin kwanton bauna da ’yan bindigar suka shirya kaiwa yankin.

Kwamishinan ya ce, gwamnan Kaduna ya bayyana gamsuwa bisa ci gaban da aka samu, kana ya bukaci sojojin da su ci gaba da aiki tukuru don cimma nasarar kawo karshen ayyukan ’yan bindigar. (Ahmad)