logo

HAUSA

Adadin tasoshin 5G da aka gina a kasar Sin ya kai miliyan 1.159

2021-10-20 10:21:23 CRI

Adadin tasoshin 5G da aka gina a kasar Sin ya kai miliyan 1.159_fororder_5G

Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar jiya Talata sun nuna cewa, harkokin masana’antu da sadarwa na kasar sun samu ci gaba yadda ya kamata a cikin rubu’in ukun farkon bana.

Kakakin ma’aikatar, kuma shugaban hukumar sa ido kan ayyukan masana’antu da sadarwar kasar Luo Junjie, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labaran da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira jiya da cewa, kwatankwacin adadin ayyukan sadarwa na kasar ya karu da kaso 28 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, haka kuma adadin kudin shiga da aka samu a bangaren ya karu da kaso 8.4 bisa dari, a cewarsa:

“Kawo yanzu, gaba daya adadin tasoshin fasahar 5G da aka gina a fadin kasar Sin ya kai miliyan 1 da dubu 159, kuma adadin iyalai da suke amfani da fasahar ya kai miliyan 450, kana ayyukan masana’antun dake shafar fasahar 5G da ake ginawa a kasar sun kai sama da 1800.”

Luo Junjie ya kara da cewa, duk da cewa, matsalar karancin masarrafar kwanfuta tana kawowa sana’ar kera motoci tasiri, amma an yi hasashe cewa, za a saukaka matsalar a cikin watanni ukun karshen bana. (Jamila)