Yadda tsarin sufuri mai dorewa zai inganta makomar bil-Adama
2021-10-20 11:02:43 CRI
A ranar Asabar 16 ga watan Oktoban wannan shekara ce, aka kammala taron kasa da kasa kan sufuri mai dorewa na MDD karo na biyu, har ma aka fidda sanarwar Beijing wadda ta jaddada muhimmancin tsarin sufuri mai dorewa, da alfanun gaggauta yin sauye-sauye da nufin cimma nasarar sufuri mai dorewa a matsayin wani muhimmin ginshikin da zai samar da kyakkyawar makoma ga bil Adama baki daya.
A cewar sanarwar, idan aka yi amfani da sabbin fasahohin zamani yadda ya kamata, hakika za su kasance a matsayin jigon da zai warware kalubaloli masu yawa dake shafar sufuri mai dorewa. Sanarwar ta kuma ba da kwarin gwiwa game da hadin gwiwar kasa da kasa, da samar da kwarewa da musayar ilmi a tsakanin kasashen duniya.
Haka kuma, akwai bukatar magance yanayin da ake ciki a yankunan karkara da wasu kasashen dake cikin yanayi na musamman ta hanyar fadada tsarin sufuri mai dorewa da ababen more rayuwar jama’a. Sannan ya kamata a kara kokari wajen kiyaye aukuwar haddura a hanyoyin mota, kuma a inganta tsarin kandagarkin annoba da matakan da ake dauka na kai dauki a fannin sufuri.
Mahalarta taron sun yi maraba da kafa cibiyar kirkire-kirkire da musayar ilmi ta kasa da kasa a fannin sufuri mai dorewa a kasar Sin, wacce za ta mayar da hankali wajen musayar ilmi da samar da kwarewa a kasashe masu tasowa.
A yayin jawabinsa yayin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kafa tsarin tattalin arziki na neman samun ci gaba, ta hanyar rage gurbata iska da inganta bunkasuwar tattalin arziki, da zaman al’umma, ta hanyar tsimin makamashi, dabaru ne na dogon lokaci, don samun ci gaba mai dorewa.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a kara zuba jari a harkokin sufuri a yankunan da ke fama da talauci, ta yadda tattalin arziki da rayuwar jama'a a yankunan za su bunkasa. Kana ya zama dole a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa, da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da kara ba da tallafi ga kasashe mafi karancin ci gaba, da kasashe masu tasowa da ba sa kusa da ruwa, a fannin gina manyan kayayyakin sufuri, ta yadda za a samu wadata tare. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)