Abinci Tushen Rayuwa
2021-10-20 16:42:51 CRI
A ranar 16 ga watan Oktoba ne, aka yi bikin ranar samar da abinci ta duniya, wadda MDD ta kan kebe a kowa ce shekara, don nazartar irin nasarori da ma akasin haka da bangaren aikin samar da abinci a duniya ke fuskanta. Sai dai annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta haifar da illoli da sauran matsaloli ga bangaren samar da abinci a duniya, inda alkaluma ke nuna cewa, kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa.
Sai dai yayin da wasu kasashe ke nuna halin ko’in kula kan wannan lamari, ita kuwa kasar Sin a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ganin duniya ta amfana da duk wata irin kwarewa da fasahohinta, musamman kasashe masu tasowa, ta dade tana taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta ayyukansu na noma ta hanyoyi daban daban.
Bayanai na nuna cewa, daga lokacin da aka kaddamar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin hukumar samar da abinci da gona ta MDD wato FAO, a shekarar 1996, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tura masana ayyukan gona da injiniyoyi kusan 1100 zuwa kasashe sama da guda 40 na nahiyar Afrika, da Asiya, da kudancin Pacific, da yankin Caribbean da sauran sassan duniya.
Karkashin kulawar hukumar FAO, kwararrun na kasar Sin sun yi aiki tukuru wajen daga matsayin fasahohin ayyukan noma sama da 1000 a kasashe masu yawa a fannoni daban daban na aikin gona, da kiwon dabbobi da halittun ruwa, da noman rani, da kuma sarrafa kayan amfanin gona, lamarin da ya taimaka wajen bunkasa karuwar samar da irin shuka a gonaki daga kaso 30% zuwa 60%. Haka kuma kusan manoma 100,000 a kasashen duniya ne suka samu irin wannan horo daga masanan na kasar Sin.
Bikin na bana dai, ya zo a gabar da duniya ke fama da tasirin annobar COVID-19, baya ga matsaloli na sauyin yanayi dake shi ma ke yiwa bangaren aikin gona illa ta wasu fannoni. Sai dai kamar kullum, bikin magaji ba ya hana na magajiya, ma’ana hakan ba zai hana masu ruwa sa tsaki daukar matakan da suka dace na ganin an wadata duniya da abinci ba.
Wani rahoton MDD game da matsalar abinci na nuna cewa, kaso 17.2 cikin 100 na al’ummar duniya ko mutane miliyan 1.3 ba sa iya samun abinci mai gina jiki da ma isasshen abinci. A bangaren yara kuwa, rahoton ya ce, tun a shekarar 2012, babu wani ci gaba da aka samu wajen matsalar karancin nauyin jariran da aka haifa.
Duba da irin wadannan matsaloli da ma alkaluman da muka zayyana a sama, ya sa masu fashin baki ke cewa, manufar wannan rana ita ce, fadakar da jama’a game da mutanen da ba su da sukunin samun abincin da za su kai ga bakin salati ganin cewa, akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai. Don haka, akwai bukatar amfani da irin wannan rana, don kara ilimantar da jama’a da wadanda alhakin magance wannan matsala ya rataya a wuyansu game da muhimmancin abinci, tare da taimakon kasashe da ma al’ummomin da ke matukar bukatar abinci domin toshe uwar hanji. (Ibrahim Yaya)