logo

HAUSA

Mene ne sojojin Amurka suka yi cikin dakunan gwajin halittu? Muna jiran bayanin Amurka!

2021-10-19 13:25:28 CRI

Mene ne sojojin Amurka suka yi cikin dakunan gwajin halittu? Muna jiran bayanin Amurka!_fororder_gwajin halittu

Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta riga ta kafa dakunan gwajin halittu sama da guda 200 a sassan duniya, kuma, an gina wasu daga cikinsu bisa goyon bayan ma’aikatar tsaron kasar.

Kamar a kasar Kazakhstan, rundunar sojan kasar Amurka ta samar da taimakon kudi wajen gina cibiyoyin gwajin halittu guda 6. Kuma, bisa bayani mai taken “Dakunan gwajin halittu na kasar Amurka dake kasar Kazakhstan” da aka fidda a shafin yanar gizo na “Nazarin siyasa da harkokin soja” na kasar Rasha, an ce, a karkashin goyon bayan kasar Amurka, an gudanar da shirin KZ-33 a dakin gwajin dake birnin Almaty na kasar Kazakhstan a shekarar 2017, inda masu nazari suka tattara samfurin kasusuwan jemagu dari 2 daga ramuka guda uku a jihar Turkistan ta kasar Kazakhstan, inda suka gano nau’o’i 12 na kwayoyin cutar COVID-19. Wasu masanan kasar Kazakhstan suna ganin cewa, shirin KZ-33 da rundunar sojan kasar Amurka ta aiwatar shi ne asalin yaduwar cutar COVID-19.

Bayan kafofin yada labarai na kasashen duniya sun bankado mugun gwaje-gwajen da rundunar sojan kasar Amurka ta yi cikin dakin gwajin halittu na Fort Detrick, da dakin gwajin halittu na Baric na jami’ar North Carolina da kuma wasu dakunan gwajin halittu dake kasashen ketare, al’ummomin kasashen duniya sun fara kira ga kasar Amurka da ta yi bayani kan “yadda rundunar sojanta ta yi nazari kan kwayoyin cuta cikin dakunan gwajinta”.

Shi ya sa, bai kamata gwamnatin kasar Amurka ta ci gaba da yin shiru kan wannan batu ba, kuma, ya kamata ta yi cikakken bayani domin biyan bukatun al’ummomin kasa da kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)