logo

HAUSA

Sinawa na burin farantawa al’ummar duniya

2021-10-18 17:26:07 CRI

Sinawa na burin farantawa al’ummar duniya_fororder_1018-01

Har kullum shugabanci na gari yana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tunanin al’umma tare da dora su bisa turba ta gari don samun ci gaba da kuma more zaman rayuwa cikin lumana. Rayuwar bil Adama tana kasancewa mai dadi da annashuwa ne yayin da al’ummar ke rayuwa cikin zaman jituwa da takwarorinsu na cikin gida da makwabtan da ma na sauran sassan duniya. A mabambantan lokuta shugabanni da jagororin kasar Sin sun sha bayyana aniyar kasar wajen kokarin kyautata zaman rayuwar al’umma da samar da makomar bai daya ga dukkan bil adama. Har kullum babban burin masu rike da madafun iko a kasar Sin shi ne kokarin neman kyautata mu’amala da al’ummun kasa da kasa domin a gudu tare a tsira tare. Alal misali, kan wannan batu, a kwanakin baya babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS ya bayyana burin al’ummar Sinawa na ganin al’ummun duniya suna rayuwa cikin farin ciki da walwala. A cewar shugaba Xi Jinping, kasar Sin ba kawai tana bukatar samun zaman lafiya da hadin kan al’ummarta ba ne, har ma tana burin ganin zaman lafiya da lumana sun wanzu a dukkan kasashen duniya domin samun ci gaba na bai daya. Xi ya yi wannan tsokaci ne yayin gabatar da jawabi a taron murnar cika shekaru 110 da juyin jiya halin shekarar 1911. Har kullum masu hikimar magana na cewa “Abin da babba ya hango yaro ko ya hau kololuwar bishiyar rimi ba zai hango ba.” Wannan kuwa ya yi daidai da kalaman shugaban inda furta cewa, tayar da tarzoma da mulkin danniya baya daga cikin dabi’un Sinawa. Burin al’ummarmu shi ne cimma nasarar bunkasa ci gaban kasa, ban da wannan ma Sinawa suna burin ganin dukkan al’ummun duniya sun yi zaman rayuwa ta farin ciki da lumana." Shugaban na Sin ya ce, zangon tafiyar da aka sanya gaba shi ne, kasar Sin a koda yaushe za ta ci gaba da kafa tutar wanzar da zaman lafiya, da bunkasuwa, da hadin gwiwa, da cin moriyar juna, da tsayawa tsayin daka wajen gina tsarin ci gaban al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama, da kuma kokarin inganta salon shugabancin duniya. (Ahmad Fagam)