Sin tana fatan kasashe masu ci gaba za su dauki matakai don nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen yaki da cutar COVID-19
2021-10-18 20:52:14 CRI
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, Sin tana fatan kasashe masu ci gaba za su dauki kwararan matakai don tallafawa kokarin kasashe masu tasowa wajen yaki da cutar COVID-19, da samar da gudummawa wajen kyautata tsarin kiwon lafiyar jama’a na duniya.
Rahotanni na cewa, kasar Italiya wadda ke jagorancin kungiyar G20 a wannan karo, tana shirin kafa kwamitin tattara kudi na kiwon lafiya na duniya da asusun musamman a wannan fanni, wanda ya samu cikakken goyon baya daga membobin kungiyar G20, amma Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar BRICS sun ki amincewa da wannan.
Game da wannan batu, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, Sin ta goyi bayan kungiyar G20 da ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma daidaito da yin hadin gwiwa kan kiwon kafiya a duniya. Amma bai kamata a rage ikon hukumar kiwon lafiya ta duniya da ayyukan sarrafa harkokin kiwon lafiya na duniya da hukumar ta gudanar. Harkokin kiwon lafiya na duniya suna shafar moriyar kasa da kasa, ya kamata a kara sauraron ra’ayoyin kasa da kasa musamman kasashe masu tasowa, da tattauna shirin a tsakanin dukkan mambobin hukumar kiwon lafiya ta duniya. (Zainab)