logo

HAUSA

Sakatariyar zartaswar ESCAP: Sin ta ba da babbar gudummawa ga ci gaban MDD cikin shekaru 50

2021-10-18 10:53:46 CRI

Sakatariyar zartaswar ESCAP: Sin ta ba da babbar gudummawa ga ci gaban MDD cikin shekaru 50_fororder_1018

Kwanan baya sakatariyar zartaswar hukumar zamantakewar al’umma da tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik ta MDD wato ESCAP a takaice, madam Armida Salsiah Alisjahbana ta zanta da wakilin CMG, inda ta bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da suka gabata, kasar Sin ta ba da babbar gudummowa ga ci gaban MDD, inda ta ba da jagoranci a fannoni daban daban.

Madam Alisjahbana ta kara da cewa, kasar Sin daya ce daga cikin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik wadanda suka samu ci gaba cikin sauri, dalilin haka shi ne, tana gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya a fannoni da dama, kuma tana rike da huldar abokantaka tare da su, a cewarta:

“Har kullum hukumar zamantakewar al’umma da tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik ta MDD, tana matukar kokari wajen ingiza hada kai tsakanin kasashen duniya, inda kasar Sin take ba da babbar gudummowa game da hakan. A ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan aikin hukumar. Alal misali, a fannonin tsara manufar samar da isasshen abinci, da tsara manufar dakile sauyin yanayi, da rage gurbatacciyar iska, kana kasar Sin ta ba da jagoranci a wasu fannoni, musamman ma wajen yaki da talauci, da raya nau’o’in makamashin da ake iya sake amfani da su.”(Jamila)