logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 a shiyyar arewacin kasar

2021-10-15 10:41:10 CMG

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 a shiyyar arewacin kasar_fororder_211015-Najeriya2-Ahmad

A kalla ‘yan bindiga 45 aka kashe a ayyukan farautar masu garkuwa da mutane wanda dakarun sojojin kasar suka kaddamar a karo da daban daban, kamar yadda hukumar sojojin kasar ta bayyana.

Bernard Onyeuko, kakakin hukumar sojojin Najeriya, ya bayyanawa ‘yan jaridu a Abuja cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kama wasu ‘yan fashin kimanin 60 a shiyyoyin arewa maso yammaci da arewa ta tsakiyar Najeriyar a makonni biyun da suka gabata.

Onyeuko ya ce, ayyukan samamen da sojojin ke gudanarwa a yankin arewacin kasar wani gagarumin aiki ne na farautar ‘yan bindiga wadanda aka fi sani da ‘yan fashin daji, da suke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Kakakin sojojin ya bayyana cewa, dakarun sojojin sun yi nasarar mamaye muhimman wuraren da ‘yan bindigar ke aikata laifuka kana suna cigaba da kaddamar da zafafan hare hare bisa taimako da hadin gwiwar sojojin sama, inda suka ceto fararen hula hudu da aka yi garkuwa da su.(Ahmad)

Bello