logo

HAUSA

Sin ta ba da tabbaci ga zaman rayuwar tsoffi

2021-10-15 21:46:29 CRI

Sin ta ba da tabbaci ga zaman rayuwar tsoffi_fororder_微信图片_20211015214603

Lokacin da nake makaranta, na taba ziyartar wani gidan tsoffi don ba su kulawa, inda na duba wata wakar da suka rubuta a jikin bango, wadda ta bayyana kuzarinsu da kuma yadda suke jin dadin zaman rayuwarsu. Ko shakka babu, rayuwar tsoffi a nan kasar Sin na da nishadi matuka, baki da dama na sha’awa matuka kan yadda tsoffi ke raye-raye a lambunan shan iska, hakika hakan wata hanya ce da tsoffi suke bi don motsa jiki da tuntubar juna a tsakanin abokai a nan kasar, inda tsoffi suka sanya riguna masu kyaun gani, suke raye-raye tare da wakoki, kuma farin ciki na bayyana a kan fuskokinsu. Wannan shi ne dalilin da ya sa wasu baki sun yi ihu cewa: Zan so in zama a kasar Sin bayan na tsufa.

Ranar 14 ga wata, bikin gargajiya da ake kira Chongyang na kasar Sin ne, bikin da ke da ma’anar girmamawa tsoffi, a wannan rana kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin tabbatar da wasu tsare-tsare dangane da tsoffi, don su cin gajiyar ci gaban kasar, tare da gaida tsoffi a wannan rana. To, daga nan kuna iya ganin cewa, tsoffin kasar Sin na iya more rayuwarsu yadda ya kamata don gwamnati ta baiwa musu tabbaci daga dukkan fannoni.

Ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan cibiyoyi masu kula da tsoffi ya kai dubu 38 a nan kasar, inda ake kulawa da tsoffi miliyan 4.831, wannan adadi zai ci gaba da karuwa nan gaba, don biyan bukatun tsoffin da ke da wannan bukata. Ban da wannan kuma, yawan Sinawa da suke shiga inshorar ba da tabbaci ga rayuwar tsoffi ya kai miliyan 999, abin da ya nuna cewa, yawancin tsoffi na iya samun tabbaci. Hakazalika, an shigo da tsoffi masu fama da zaman rayuwa mafi kankanta da yawansu ya kai miliyan 18.34 cikin tsarin inshora, har kuma gwamnatin ta baiwa tsoffi mafi fama da mawuyancin hali da yawansu ya kai miliyan 4.08 tallafin kai tsaye. Dadin dadawa, dukkanin larduna na fitar da manufofin gatanci na tallafawa tsoffi a cikin rayuwarsu, alal misali, tsoffi ‘yan sama da shekaru 60 da haifuwa za su iya shiga lambunan shan iska da ma motocin bus ba tare da biyan kudi ba, haka kuma an yin musu rigakafin wasu cututtuka kyauta.

Ranar 25 ga watan Fabrairu, a bikin karrama mutanen dake ba da gudunmawar wajen kawar da talauci, lokacin da tsofuwa Xia Sen wadda ke da shekaru 98 a duniya tana kokarin tsayawa don karbar lambar yabo daga hannun shugaba Xi Jinping akan kujerar guragu, Xi Jinping ya hana mata tsayawa ya sunkuya mika ta lambar yabon, abin da ya burge mutane da dama. A farkon wannan bayani, na gaya muku cewa, na taba zuwa gidan tsoffi don basu tallafi, a hakikka dai, duk daliban makaranta suna aikata hakan a ko wace shekara, abin da ya bayyana cewa, al’ummar Sinawa tun daga shugaba har zuwa yara suna girmamawa tsoffi matuka, abin da ya zama al’adar kasar Sin, ban da wannan kuma a wani bangare gwamnatin Sin tana aiwatar da nagartattun manufofin tallafawa tsoffi, matakin da ya kara ba da tabbaci ga tsoffi.

Na taba tambayar mamata cewa, yanzu shekarunki ya kai 60, ko za ki shiga masu raye-raye a lambunan shan iska? Mamata ta gaya min cewa: “A ganina shekaru 60 da haifuwa bai kai zama tsoffi ba, zaman al’umma na saurin bunkasa, lokacin da na tsufa za a kara bullo da wasu abubuwa masu ban sha’awa ga tsoffi don samar musu nishadi da walwala.”(Amina Xu)