Jama’ar Kasar Sin Suna More Tsarin Demokradiyya Na Ainihi
2021-10-15 15:26:23 CRI
Shugaban kasar Sin ya gabatar da tunanin aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya, don tabbatar da jama’ar kasar sun more tsarin demokradiyya na ainihi, da biyan bukatunsu, wanda yake da alamar musamman ta kasar Sin. Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron nazarin aikin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da aka gudanar a kwanakin baya,
Kasa da kasa suna iya ganin cewa, Sin tana da cikakken tsari kan yadda take aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya, kana ana aiwatar da tsarin a dukkan fannoni. Tsarin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin tsari ne da ake amfani da shi don cimma burin aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya, da tabbatar da jin ra’ayoyin jama’a a dukkan ayyukan gwamnati yayin da jam’iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar suke tsara manufofi, da aiwatar da ayyuka, da kuma sa ido kan ayyukan.
Mashahurin masanin tsarin dokoki na kasar Masar Shawki al-Sayyid ya yi nuni da cewa, Sin ta samu gagarumin ci gaba, lamarin da ya shaida cewa, aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya yana da amfani, duba da yadda ya sa kaimi ga samun ci gaba a kasar, tare da kirkire-kirkire a tsakanin jama’ar kasar.
Ana iya ganin cewa, hanyar siyasa bisa tsarin demokuradiyya ta musamman da kasar Sin take takawa tana da amfani sosai. A nan gaba, Sin za ta ci gaba da bin wannan hanya, da kara samar da gudummawa ga samun ci gaba kan harkokin siyasa ga dukkan dan Adam. (Zainab)