logo

HAUSA

Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan BH 29

2021-10-15 10:44:58 CMG

Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan BH 29_fororder_211015-Najeriya3-Faeza

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarunta sun kashe jimillar mayakan BH 29 a baya-bayan nan a yankin arewa maso gabashin kasar, biyo bayan wasu jerin samame da suka kai.

Kakakin rundunar Bernard Onyeuko, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an kuma kama wasu ‘yan kungiyar 13 da suka hada da masu taimaka musu da masu kai tsegumi, yayin da dakarun suka matse kaimi wajen kai farmaki kan kungiyar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, cikin makonni biyu da suka gabata.

Tun daga watan Yunin bana zuwa yanzu, jimilar mayakan BH da iyalansu 13,243 ne suka mika wuya ga dakaru a yankin. Ya kara da cewa, wannan ya biyo bayan hare-haren da dakarun suke kai musu.

A cewarsa, jerin farmaki ta kasa da sama da rundunar ke kai wa wurare daban-daban a fadin yankin arewa maso gabashin kasar ya kai ga rage karfin kungiyar wajen kai hare-hare. (Fa’iza Mustapha)

Faeza