logo

HAUSA

Kwararru: Hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin makamashi da masana’antu muhimmin ne wajen farfadowa daga annoba

2021-10-14 10:24:56 CRI

Kwararru: Hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin makamashi da masana’antu muhimmin ne wajen farfadowa daga annoba_fororder_1014-ahmad-3-Sin da afirka

Wani kwararre ya bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika a fannonin makamashi da masana’antu muhimman ginshikai ne wajen gaggauta farfadowa daga barnar da annobar COVID-19 ta haifar, kwararran ya bayyana hakan a wani taron dandali wanda aka gudanar a Nairobi, babban birnin kasar Kenya a ranar Laraba.

Kirimi Kaberia, babban sakatare a hukumar bunkasa masana’antun kasar Kenya, ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su karfafa hadin gwiwarsu da kasar Sin don cimma burinsu na samun ingantaccen makamashi da bunkasa masana’antunsu na cikin gida.

Ya ce hadin gwiwar Sin da Afrika a fannonin masana’antu da makamashi yana da matukar muhimmanci wajen samun ci gaba, da daidaito da farfadowa bayan kawo karshen annobar COVID-19 domin samun dorewar dadaddiyar alakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad)