logo

HAUSA

‘Yar wasan kwallon kafar Syria ta yi rawar gani duk da rashin samun tagomashi daga sassan kasa da kasa

2021-10-14 12:35:03 CRI

‘Yar wasan kwallon kafar Syria ta yi rawar gani duk da rashin samun tagomashi daga sassan kasa da kasa_fororder_1014-01

Rona Murad Ayzouk mai shekaru 22 da haihuwa, ta shafe tsawon lokaci tana buga kwallon kafa, tana da kwarewa wajen sarrafa kwallo da sauri da kuzari, inda har ta kai ga karya matsayin bajimta na duniya wajen bajimtar sarrafa kwallo, amma duk da haka ba ta samu jan hankulan duniya sosai ba.

A filin wasa na Al-Jalaa dake birnin Damascus, Ayzouk ta shafe lokaci mai tsawo tana samun horo, da itisayen sarrafa kwallo. Matashiyar wadda ke karatun injiniyan tsara gine gine, ta fara sha’awar kwallon kafa ne daga mahaifin ta, wadda ke aikin horas da ‘yan kwallo.

Ana iya cewa sha’awar kwallon kafan ta ya samo asali ne daga iyalin ta. Kafin a haifi Ayzouk, mahaifanta sun yi fatan sanyawa jaririn su suna Ronaldinho, wato sunan shahararren dan kwallon kafar nan na Brazil. Yayin da suka haifi mace, sai suka ciri haruffa 4 na farkon sunan dan wasan suka sanya mata. Wato suka sa mata suna Rona.

Ayzouk Rona na cikin matasan ‘yan wasan kwallon kasar Syria dake rayuwa madaidaiciya bakin gwargwado, a kasar da yaki ya daidaita cikin shekaru sama da 10, kuma kawo yanzu kasar ke ci gaba da fuskantar kalubale daban daban.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, matashiyar wadda ke yawo ko ina rike da kwallo kafa, ta ce tana kallon nau’oin bidiyo kala kala a yanar gizo domin koyon dabarun kwallon kafa, tun bayana da ta fara taka leda a kwalejin koyon kwallo dake kasar shekaru 8 da suka gabata.

A baya bayan nan, tana kara sha’awar ta ga fannin sharrafa kwallo, a yayin da kocin ta ke aika mata da bidiyon dabarun kyautata fasaha a fannin, tana kuma umartar ta data rika daukar na ta bidiyon don karfafa gwiwar masu sha’awar  kwallo a yayin da ake zaman kullen COVID-19.

Ta ce "Har kullum ina kallon bidiyo domin koyon sabbin dabaru da hikimomin mata masu taka leda. Ina matukar sha’awar yadda ake sarrafa kwallo, na kuma yi imanin cewa, ina da basira wadda zan so karrafawa da kuma bunkasa ci gaban ta.

Kocin ta wadda ita ma mace ce, ta lura da yadda wata ‘yar wasan kasar hadaddiyar daular larabawa ta karya matsayin bajimta a fannin sarafa kwallo, inda take fatan Ayzouk za ta yi kokarin ganin ta zarce wannan ‘yar wasa, a dabarun da za ta gwada a cikin bidiyon ta. Ba tare da bata lokaci ba kuma, Ayzouk ta fara gwada na ta fasahohi har ta kai ga cimma nasara.

Ayzouk ta ce "Na yi nasarar karya matsayin bajimtar Guinness wanda ‘yar wasan kasar hadaddiyar daular larabawa ta kafa, inda ta ci kwallaye 86 ta hanyar dabarun sarrafa kwallo daban daban cikin minti daya. A nawa gwajin na ci kwallaye 93 cikin dakika 40.

Wannan nasara da matashiyar ‘yan Syria ta cimma ta kuma nada a bidiyo, ta ja hankulan kafafen watsa labarai a ciki da wajen Syria, suna masu fatan za ta yi nasarar shigar da tarihin ta cikin kundin nuna bajimta na duniya na Guinness, sai dai hakan ba ta samu ba.

Wata matsala da ta gamu da ita ita ce, ba wanda ya iya taimaka mata, kamar yadda kocinta ta bayyana, wato saboda annobar COVID-19 da ake fuskanta da kuma tashe tashen hankula a Syria, ba wasu tawaga na kasa da kasa da za su iya shiga Syria domin dubawa da jinjinawa kwazon ta, a matsayin wadda ta karya matsayin bajimtar sarrafa kwallon kafa.

Ayzouk bata ji dadin hakan ba, kasancewar dole ta dogara da kan ta kadai wajen cimma nasarorin da ta sa gaba. Ta ce duk da yanayin da ake ciki a Syria, ba za ta taba yin watsi da burikan ta, da nasarorin da ta sanya a gaba ba.

Ayzouk ta kara da cewa "Yanayin fannin wasanni a Syria yayi muni matuka. Amma duk da haka, ina dogaro da kai na, ina kuma samun horo da burin al’amura za su kyautata nan gaba. Ina aiki tukuru domin kara samun gogewa, ban samu goyon baya ba, dole nayi iya kokari, saboda ina son wannan wasa kuma ba zan taba barin yin sa ba.

Matashiyar ‘yar kwallon ta ce matasan kasar Syria na yanzu, suna cimma nasarori ne ba tare da samun taimakon wani ba, kana ba bu mai yaba musu. Suna kara yin gaba da fatan cimma burikan su na rayuwa, a kasar da take shan fama da tashe tashen hankula da takunkuman kasar Amurka, wadanda ke shafar rayukan ‘yan Syria ta fannoni da dama, sun kuma yi mummunan tasiri ga makomar matasan kasar na yanzu.

Ayzouk ta ce "Muna fuskantar matsin lamba mai yawa. Takunkuman da aka kakabawa kasar mu sun yi matukar shafar mu, sun kuma tsayar da harkoki gaba daya, wanda hakan ya dakile burin mu na cimma manyan nasarori da kara yin gaba, ko haskaka nasarorin mu a idanun duniya.

Ayzouk ta ce, abun takaici ne ganin yadda matasan Syria suke fuskanci kalubale na rashin nuna musu kulawa, wadda za ta ba su zarafin kaiwa ga cimma nasarorin da suke fata.