logo

HAUSA

Rukuni na 9 na tawagar jami’an lafiyar Sin ta fara aiki a Sudan ta kudu

2021-10-14 14:02:52 CRI

Rukuni na 9 na tawagar jami’an lafiyar Sin ta fara aiki a Sudan ta kudu_fororder_1014-ahmad-5-likitocin Sin

A yanzu haka rukuni na tara na tawagar jami’an kiwon lafiyar kasar Sin ta isa kasar Sudan ta kudu har ma ta fara aiki a kasar mafi yarinta a duniya.

Isaac Maker, daraktan asibitin koyarwa na Juba, inda a can ne tawagar masana kiwon lafiyar kasar Sin ta yada zango, ya yabawa dukkan tawagogin lafiyar wato tawagar jami’an kiwon lafiyar kasar Sin da ta kammala aikinta da kuma sabuwar tawagar da ta isa kasar a halin yanzu bisa irin gagarumar gudunmawar da suke baiwa fannin kiwon lafiyar kasar Sudan ta kudu.

Tawagar ta 9 wacce ta tashi daga lardin Anhui na gabashin kasar Sin, ta isa Sudan ta kudun a ranar 6 ga watan Satumba, inda ta maye gurbin tawaga ta takwas ta jami’an kiwon lafiyar kasar ta Sin.

Maker ya bayyana cewa, zuwan tawagar likitocin kasar Sin ya taimakawa jami’an kiwon lafiyar kasar Sudan ta kudu wajen inganta tsarin ayyukansu, baya ga taimaka musu wajen samun ingantaccen ilmi da kwarewa.

Likitocin kasar Sin sun shafe shekaru da dama suna gudanar aikin ba da jinya ga marasa lafiya da kuma ba da horo ga likitocin kasar Sudan ta kudun tun bayan kasar ta samu ’yancin kai a shekarar 2011. (Ahmad)