logo

HAUSA

Somalia ta ce tattalin arzikinta na farfadowa duk da tasirin COVID-19

2021-10-14 10:49:37 CRI

Somalia ta ce tattalin arzikinta na farfadowa duk da tasirin COVID-19_fororder_1014-ahmad-4-Somaliya

Babban bankin kasar Somalia ya ce, ana sa ran tattalin arzikin kasar zai bunkasa sannu a hankali duk da mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar, wanda ya yi matukar shafar kasar a rubu’i na uku da na hudu na shekarar 2020.

Babban bankin Somaliya (CBS), ya bayyana a ranar Laraba cewa, ana hasashen samun karuwar GDPn kasar da kashi 2.4 a shekarar nan ta 2021, sabanin kashi 0.3 a shekarar 2020 sanadiyyar matakai da aka dauka domin dakile annobar COVID-19 da suka hada da kafa dokar kulle ga kuma bala’in farin dango da kuma fari.

A cewar bakin, an samu sassauci game da tashin farashin kayayyaki inda har yanzu yana daidai da na lokacin rubu’i na daya na wannan shekara, haka zalika, kasuwar hada hadar kudi ma ta dan daidaita a mafi yawan shiyyoyin kasar Somalia. (Ahmad Fagam)