logo

HAUSA

Sin na dora muhimmanci sosai ga rayuwar tsofaffi

2021-10-14 15:12:37 CRI

Sin na dora muhimmanci sosai ga rayuwar tsofaffi_fororder_A

Yayin da kasar Sin ke bikin girmama tsofaffi na shekara shekara a tsakiyar makon nan, ko bikin “Chongyang” da harshen Sinanci, mahukuntan kasar sun jaddada muhimmancin samar da ingantacciyar rayuwa ga tsofaffi.

A wannan gaba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban na kasarsa, da su kara azama wajen hidimtawa tsofaffi, da kirkiro karin sabbin tsare-tsare, da manufofi, da shigar da isassun kudade, musamman batun samar da inshora, ta yadda wannan muhimmin aiki zai kara ingantuwa.

Sanin kowa ne dai cewa, rayuwa wata da’ira ce ga dukkanin dan Adam, wato daga haihuwa zuwa tsufan sa, kuma kamar yadda matasa ke zama ginshiki na gina rayuwar al’ummun su, bayan wani lokaci matasan kan zarce wannan gaba ta karfin jiki zuwa lokaci na tsufa, a kuma wannan lokaci, dan adam na bukatar karin kulawa, daga makusanta da al’umma baki daya.

Kaza lika masharhanta da dama na sanya tsofaffi cikin rukunin masu rauni a al’umma, kamar dai yara kanana, don haka ne ake da bukatar ba su kulawa ta musamman, da kauna da girmamawa.

Idan muka yi duba da nau’o’in hidimomi na kula da rayuwar tsofaffi da kasar Sin ta tanada, wadanda kuma ake aiwatarwa yadda ya kamata, da ma wadanda ake tsarawa domin gaba, abu ne a zahiri cewa, mahukuntan Sin ba su manta da tsofaffi ba, a manufofin kasar na samar da ingantacciyar makomar bil adama ta bai daya.

Fatan dai shi ne, al’ummun duniya za su kara maida hankali ga martaba muhimmiyar gudummawar ciyar da kasa gaba, wadda dattijai a dukkanin sassan duniya suke bayarwa, kana a ci gaba da baiwa tsofaffin kulawa, musamman a fannin ingancin kiwon lafiyar su, kuma har kullum a rika tunawa da gudummawar da suka bayar yayin kuruciya. (Saminu Hassan)